Duk me yin YouTube ya kamata yasan wannan garabasar
Ko kunsan YouTube zasu bawa masu amfani da manhajar tasu kyautar zunzurutun kudi har $ 1000 ga wanda suke da YouTube channel tasu kuma suke sanya kirkirarsu a kai.
A ranar laraba ne dai aka fitar da sanarwar cewar za'a biya masu YouTube din kansu kudi har kimanin dollar dubu daya a wani tsari da ake kira YouTube next up, wanda za'a wari wasu daga cikin YouTubers da channel dinsu ta cika sharadin wasu matakai domin a tallafa musu da kudi dollar dubu daya domin su inganta harkar channel din tasu.
An fitar da sunan Nigeria da kuma south Africa a matsayin sune kasashen da za suci gajiyar wannan tallafin da za'a bayar din.
An fitar da tsarin ne domin taimakawa masu kananan karfi a harkar ta YouTube din domin su samu damar sake gyara harkar tasu, su kuma tsarata kamar yadda agent dinsu ya fada.
Sannan yace bawai duk wani mai YouTube channel dinne zai samu wannan garabasar ba a'a sai wanda yake da rabo kuma ya taka matakin da suke bukata shine kadai zai amfana da tallafin dollar dubu dayan bayan sun gabatar da horo akan sanin makamar aiki kuma mutanen sun samu kwarewa a tsarin gamayyar bada horo ta YouTube next up din.
Wannan tsarin na YouTube next up din kowa yanada damar shiga matukar subscribers din channel dinsa sunkai dubu goma zuwa sama.
Sannan kuma akwai video a kalla guda uku masu kyau wanda mai channel dinne ya dora nasa ne ko kuma muce kirkirarsa ne ba wasu ne sukai ya dauka ba na wata uku da suka wuce baya.
Sannan ya kasance channel din ta mutum bata karya dokar YouTube ba kuma ba'a dakatar da ita ba ko aka bata strike ba.
Sannan wajen cike gurin akwai bayanai kala kala wanda ake da bukatar mutum ya karanta kuma ya cike su. Sannan saboda sabanin fassara zaku iya duba tsarin cikin google domin ku sake samun cikakken bayani.
Domin shiga tsarin kai tsaye ka danna wannan blue din rubutun da zamu ajiye a kasa.
Sannan idan mutum bai fuskanci bayanin nawa ba kai tsaye zai iya rubuta YouTube next up cikin browser dinsa domin sake karanta bayanin dalla dalla.
Comments
Post a Comment