Min menu

Pages

GWAMNATIN JIHAR JIGAWA TA DAKATAR DA TUƘA BABURA DAGA ƘARFE (9) NA DARE:-

 GWAMNATIN JIHAR JIGAWA TA DAKATAR DA TUƘA BABURA DAGA ƘARFE (9) NA DARE:-



Gwamnatin Jihar Jigawa, ƙarƙashin jagorancin gwamna Muhammad Badaru Abubakar, (MON, MNI), ta dakatar da tuka Babura na haya da masu zaman kansu daga ƙarfe (9) na dare sai zuwa ƙarfe (6) na safe a kowacce rana a dukkan ƙananan hukumomin Jihar guda (27).


Shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin Jihar, kana shugaban ƙaramar hukumar Dutse, babban birnin Jihar, Malam Bala Usman Chamo shi ne ya sanar da hakan ga manema labarai a wannan rana ta Laraba.


Wannan mataki ya biyo bayan duba na tsanaki da majalissar kula da harkokin tsaro ta Jihar ta yi domin ganin an daƙile matsalar garkuwa da mutane da ke neman gindin zama a Jihar wacce da babura ake amfani wajen aikata ta.


Allah Ya taimaki Jihar Jigawa da Nageriya da kafatanin shugabanninmu a kowane mataki. Allah Ya ba mu lafiya da zama lafiya da wadata.


Laraba, 8 ga watan Satumba, 2021.

Comments