Min menu

Pages

Hanyar da zaku gane masu tura muku fake alert idan sunzo shagon ku ko kuma gurin POS dinku

 Hanyar da zaku gane masu tura muku fake alert idan sunzo shagon ku ko kuma gurin POS dinku



Assalamu alaikum yan uwa barkanmu da wannan lokacin ya aiki ya hakurin kasancewa tare damu?


Hakika muna matukar jin dadin yadda kuke kasancewa tare damu kuma muna godiya sosai da sosai.


A yau za muyi muku bayani ne akan wata hanya da zaku kare kanku daga masu damfara ta hanyar amfani da alert na banki su karbi kudi a gunku ko su karbi kayan da kuke sayarwa cikin store dinku sannan su nuna muku alert cewar sun tura muku kudin.


Kamar yadda zamani yazo yanzu da technology yayi yawa za'a iya abubuwa da dama domin damfara dan haka muke son mu ankarar da mutane wata hanya da zasu kare kansu daga azzaluman yan damfara wanda suke amfani da fake alert wajen karbar kudi a guraren masu POS da kuma sauran shaguna.


Domin akwai Apps masu yawa da ake amfani dasu wajen tura alert kuma mutum bai isa ganewa ba idan ba yana ankare da cewar akwai irinsu ba, da zamu koyar da yadda ake yin irin wannan alert din to amma dake harkar ne sai a hankali yasa muka dakata domin wasu idan suka koya za ayi ba daidai ba.


Dan haka muka fi maida hankali wajen koyawa mutane yadda zasu kare kansu daga wannan damfarar. Domin abinda yaja hankalina naga wannan dinma ya dace na koyar shine rannan naje shagon wani mai pos na tarar an damfareshi makudan kudade da irin wannan alert din wanda banji dadi ba kuma agun na gane bashi kadai azzalumai suka damfara ba akwai mutane masu yawa dake fama da wannan damfarar daga azzaluman mutane ba.


Ga hanyar da zaka gane alert din da aka tura maka na fake ne.


√ Hanyar farko idan mutum yace ya tura muku kudi kuyi saurin duba wayarku kuga a inda banki suke tura muku sako ne na duka alert dinku, idan kuka ga cewar ba ta wannan gurin bane to gaskiya akwai damuwa.


√ Hanya ta biyu ka tabbatar kaga alert, karka yadda mutum ya nuna maka debit alert dinsa sannan yace shi an cire masa kudi kuma sauri yake kace masa ya tsaya saika gani tukun..


√ Ta uku idan yace maka ya tura sakon shi har sunyi masa alert, kai kuma bakaga credit alert ba, to kayi checking balance dinka idan har baka ga kudin ba to karka yadda.


√ Ko kuma idan mutum yace muku ya tura muku kudi harya nuna muku debit alert ku kuma baku gani ba kuma kunyi balance bai nuna muku ba watakila saboda network to kuyi amfani da application na bankin ku ku duba sakon da yace ya tura muku idan bakuga kudin ta nan ba shima karku yadda.


Hanya ta karshe da zaku bi bayan wannan na saman shine ku cire statement na bankin ku idan har mutum yace ya tura muku kudi kuma baka gani ba idan har banki ya nuna muku kudin bai shigo ba to kun tabbatar wannan mutumin dan yaudara ne.


Kuma idan ma ya tabbata fake alert ya tura muku bazai jira kuyi wadannan binciken ba zai gudu ko yace muku shikenan ya hakura yayi saurin barin shagon naku kar yaje ku gane daga karshe ku kamashi.


Mun kama mutane da yawa da irin wannan damfarar dan haka saiku kiyaye.

Comments