Ka sake ni, kuma ka biyani Naira Biliyan 5 saboda take hakkina — Nnamdi Kanu ya gayawa Buhari
Daga Wakilin Dimokradiyya Usman Salisu Gurbin Mikiya
Shugaban Kungiyar rajin Kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu, ya bukaci Babbar Kotun Jahar Abia data sanya Gwamnatin Nigeria umarni ta sake shi.
Majiyar Jaridar Dimokradiyya ta ruwaito cewa, Kanu ta hanyar lauyan shi Aloy Ejimakor, ya Kuma yi bukaci Kotu data sanya Gwamnatin Nigeria ta biyashi Naira Biliyan 5 a matsayin diyyar tauye hakkin shi da Gwamnati tayi.
Ejimakor ya bayyana haka a lokacin daya Fara Shari'a akan tabbatar da Hakkin Kanu.
A cikin sanarwar daya sanyawa hannu a ranar Talata Ejimakor, ya bukaci kotu data sanya Gwamnatin Nigeria ta saki shugaban Kungiyar IPOB Nnamdi Kanu.
Acewar Ejimakor " a yau na samo wani umarni daga Babbar Kotun Jahar Abia Wanda zai zama a matsayin wata Kara da zata sa a kare Hakkin Mazi Nnamdi Kanu, Wanda na samo a Babbar Kotun Jahar Abia.
Yayi nuni dacewa, an take Hakkin Kanu a lokacin da aka so halaka shi a Shekarar 2017 bayan bada shi beli, da Kuma kamashi a Kenya, tare da dawo dashi a Nigeria.
Ejimakor ya Kuma samo wani jinkai ga Kotu akan kula da Hakkin sa.
Daga cikin jinkan daya samo, Ejimakor ya bukaci kotu ta sanya Gwamnatin Nigeria taba Kanu hakuri a cikin Jama'a.
Yace dole a rubutar takardar bada hakuri a cikin jaridun Kasa.
Comments
Post a Comment