Shaikh Kabiru Gombe, Ya yi Allah wadai da Muazu magaji, kan ƙaryar da ya shirga Masa
Assalamu'alaikum
Ni Muhammad Kabir Haruna Gombe, nayi Allah wadai da karya da wani bawan Allah daga jihar Kano mai suna Muaz Magaji ya kirkira kuma ya jingina ta gareni. Kamar yadda yace nayi waya da Gwamna Mai Mala Buni akan maganar siyasa, ni tunda nake ban taba waya da Mai Mala Buni ba ko akan menene, domin wannan ba shine a gaban mu ba.
Mu ba 'yan siyasar jam'iyya bane, bamu da jam'iyya a siyasa, illa kawai muce da jama'a su zabi wanda mukewa zaton mutumin kirki ne, in zabe yazo mu cewa jama'a su zabeshi, ballatana har nayi barazanar fita daga wata jam'iyya zuwa wata jam'iyya.
Wannan karya da ya kwantara min mai hade da cin mutunci mafi kololuwa a rayuwa, sam ba'a yita ba, bamu da alaka da duk wani mai mulki da ya wuce alaka ta addini.
Dan haka mun baiwa wannan mutum mai suna Muazu Magaji awanni goma sha biyu (12hours) da ya fito ya janye maganarsa ko mu kai kara zuwa kotu, Dan Baza mu saka ido a wannan karya da ya mana tare da cin mutunci ya tafi a banza ba matukar bai fito ya karyata kansa ba.
Jama'a su kwantar da hankalin su, Tuni muka fara daukan mataki na turawa lauyoyin mu domin subi mana hakkin mu a kotu karkashin "Sashin Doka da Hukunci" na (Defamation of character) 'Bata suna ko Zubar da mutunci' "Sashi na 391 na Kundin Tsarin Laifuka da Hukunci (Penal Code).
Kuma muna da tabbacin kotu zata mana adalci wajen hukunta shi akan laifin da yayi matukar ya gagara kawo hujjojin sa akan wannan kage da cin mutunci ta yadda zai zama darasi ga 'yan baya masu hali irin nashi.
Ma'assalam
Comments
Post a Comment