Karatu kyauta a jami'ar musulunci ta Madina
Jami’ar musulunci dake madina ta sanar da bude shafinsu na internet domin daukar dalibai daga
kasashen ketare na shekarar 2021/2022 na zangon karatu.Duk dalibin dake san yasamu kyakykyawan
ilimi nagartacce tun daga karatun degree zuwa masters da PhD daga jamiar musulunci dake madina,to ana karfafar dalibai dasu nema
Karatu kyauta na jamiar musulunci ta madina dake Saudi Arabia ta hada duk abubuwan da dalibi ke bukata na harkokin kudi tun daga karatun degree,masters da kuma PhD.
Sannan scholarship din ta wadatu ne ga dalibai masu hazaka da nagartaccen ilimi na asali [educational background].
Jamiar musulunci dake madina [IU] an krkiretane a shekarar alif dari tara da sittin da daya 1961 wadda take zaune a masallaci mafi daraja na madina.
Jamiar musuluncin ta kasance ta gwamnati wadda gwamnatin ta Saudi Arabia ta kafa bugu da kari jamiar tana bada ingantaccen ilimi ga dalibanta daga dukkan sassan duniya.
TAKAITACCEN BAYANI GAME DA SHOLARSHIP DIN:
WURI: Saudi Arabia
NAU’IN DALIBAI: Undergraduate scholarship
KASASHEN DA SUKA CANCANTA: All countries [kowacce kasa]
RWARD: Cikakkiyar scholarship
LOKACIN RUFEWA: Hudu ga watan december 4,2021
KADAN DAGA SCHOLARSHIP DIN:
Dalibi me neman admission a jamiar musulunci ta madina domin karatun degree to zai cike daya daga cikin waddannan kwasa kwasan:
Electrical Engineering [shekara biyar]
Mechanical Engineering [shekara biyar]
Civil Engineering [shekara biyar]
Computer faculty
Computer Science [shekara biyar]
Information System [shekara biyar
Faculty of science
Physics [shekara hudu]
Chemistry [shekara hudu]
Mathematics [shekara hudu]
Sauran:
Shariah [islamic law] [shekara hudu]
Creed and Religions [shekara hudu]
Noble Qur’an and Islamic Studies [shekara hudu]
Arabic Language [shekara hudu]
Law System [shekara hudu]
Abubuwan da ake bukata ga dalibi
Domin cancantuwar dalibi dole yazama ya cika wadannan sharuda:
Dole dalibi ya mallaki takardar sakandare daga kasar da yake ko kuma Saudi Arabia
Yazama dalibi yana tsakanin shekara sha bakwai zuwa ashirin da biyar
Dole dalibi yabi dokokin makaranta yadda ya kamata
Dole dalibi yazama me cikakkiyar lafiya
Sannan yazama takardar kammala karatun sakandare ta kasance ta gwamnati ko ta kudi
Abubuwan da dalibai zasu amfana daga makarantar
Jamiar musulunci dake madina tana bada cikakkiyar dama ga dalibai domin samun ilimi mai inganci,ga
kadan daga abubuwan da dalibai zasu amfana:
Akwai kudi na wata wata ga dalibi [monthly stipend]
Akwai alawus na musamman ga dalaibai masu hazaka a karatu
Akwai wadataccen abinci ga daliabai a cikin makarantar
Ingantattun kayan aikin lafiya ga dalibai
Kyawawan wurin kwanan dalibai
Biyan kudin ticket ga daliabin da ya gama karatu lafiya lafiya da kuma kudin wani ticket din a duk
karshen zangon karatu na shekara
Sannan zirga zirga kyauta ne ga dalibai daga masallacin fiyayyen halitta,da kuma tafiya zuwa
aikin umrah
Akwai kayayyakin motsa jiki a cikin makarantar
Takardun da ake bukata ga dalibi:
Passport [where applicable]
Takardar haihuwa [birth certificate]
Transcript na makarantar sakandare
Da kuma takardar halin kirki [testimony of conduct]
Muhimmiyar sanarwa:
Dole dalibi ya hada duk takardun da ake da bukata,na turanci ne ko na larabci
Bayan da dalibi ya samu admission ya bada takardunsa na gaskiya zuwa ga embassy na saudia na
kasarsa.Idan kuma babu embassy a kasarsa ya kai zuwa ga hukuma wadda take sananniya ga makarantar da ya fito
Na karshe ana yawan samun matsala a bangaren bada takardu na gaskiya kama daga kan
suna,wurin haihuwa,shekarar haihuwa da sauransu,so dole dalibi ya tabbatar ya saka su dai dai
batare da wata matsalaba kafin turawa zuwa ga makarantar
Domin karin bayani a tuntubi:
Tel/920022042
Email/contact@iu.edu.sa
Website:https://iu.edu.sa/site/115
Makarantar sunayin karatun online. ( ko kuma waccece Sukeyi online din
ReplyDelete