KO ƳAN NAGERIYA ZA SU ZAƁI GWAMNA GANDUJE IDAN YA NEMI SHUGABAN ƘASA A 2023 ??
Yau Juma'a, 22 ga watan Octoba, 2021.
Tun bayan komawar Nageriya kan tsarin mulkin dimokaraɗiyya a ahekarar 1999, Jihar Kano ta yi gwamnoni guda biyu waɗanda su ka haɗa da: gwamna Kwankwaso wanda ya yi wa'adin mulki na farko daga 1999 zuwa 2003. Malam Shekarau ya karɓa ya yi wa'adin mulki biyu a jere daga 2003 zuwa 2011, sai kuma gwamna Kwankwaso ya sake karɓa ya cika wa'adin zangon mulki na biyu daga 2011 zuwa 2015.
Gwamna Ganduje shi ne gwamna na uku a yau, ya karɓi mulki a hannun Kwankwaso a shekarar 2015, bayan ya kammala wa'adin farko ya sake komawa kan kujerar a shekarar 2019 zai kuma gwamnan Kano a shekarar 2023.
Duba da irin abubuwan da ke faruwa, cikin waɗannan mutane da Jihar Kano ta yi a matsayin gwamnoni, kowannensu ya nemi shugabancin Nageriya bayan ƙarewar wa'adinsa. Yanzu abin jira a gani shi ne gwamna Ganduje, shin zai raya waccan sunar ta magabatansa gwamnoni shi ma ya fito a fafata da shi wajen neman takarar shugabancin ƙasar a 2023 ko kuwa zai zama ɗan baruwana ne ?
Shin idan gwamna Ganduje ya fito neman takarar shugaban Najeriya al'ummar Jihar Kano da ƙasar za su zaɓe shi domin ya magance matsalolin Nageriya kamar: matsalar tsaro, cin hanci da rashawa sace-sace da garkuwa da mutane da hare-haren ƴan bindiga da rashin tarbiyya da almundahana da dukiyar al'umma ? Shin ƴan Nageriya za su shirya zaɓo gwamna Ganduje idan ya nema, shin wane ƙwarin gwiwa su ke da shi a kansa cewa zai iya magance waɗannan matsalolin na Nigeria ???
Ku Bayyana Mana Ra'ayin Ku Akan Wannan Batu.
Comments
Post a Comment