Shin za'a iya satar kudi a account dinku idan aka san BVN dinku?
Anyi mana wannan tambayar yafi sau dari, mutane da dama kan tambayarmu cewar wai ana iya satar kudin mutum kawai idan ansan BVN dinsa?
To yau cikin hukuncin ubangiji za muyi muku magana akan wannan tambayar da wasu ke mana, domin mu wayar musu da kai dama sauran mutanen da muke tare dasu, wato wadanda suke biye damu cikin shafin mu.
Mecece BVN?
Bank Verification Number shine asalin rubutun idan ba'a gajarce shi ba, an kirkere ta ne a shekarar 2014 wanda aka hada gwiwa da babban bankin Nigeria wato central bank of Nigeria wanda aka sanya biomateric identification wato yadda za ayi amfani da photon yatsu domin tantance mutum, akai amfani da naura wacce daga zarar an bude maka BVN dinnan shikenan daga kasa yatsan hannunka duk wasu bayanai naka da photonka zai baiyana a jiki tun daga kan suna unguwa sunan mahaifi da kuma mahaifiya dadai sauran bayanai naka.
Sannan aka jona shi da bank wato duk lokacinda zaka bude wani account dole sai dashi, ta jikinsa ko account nawa ne dakai za'a iya gani ta jikin wannan bvn din taka.
An kirkiri wannan tsarin ne domin masu tara kudin sata a wancan lokacin, wanda hakan yasa ko mutum ya ajiye kudi a kowanne account ne za'a gani koda an tashi bincike ne.
Wannan yasa wasu daga cikin manya masu satar kudi suka rasa yadda za suyi saidai sukai kudin kasar waje ko kuma ayi musu wani guri suna boye kudin.
To magana ta gaskiya ana satar kudi ta BVN domin domin duk wanda zai iya shiga cikin BVN dinka yaga bayananka to zai iya daukar kudi a ciki kuma cikin sauki.
Dan haka muke baku shawara akan ku guji bawa mutane BVN dinku idan har baku tabbatar da yardar da kuke musu ba, sannan akwai wasu apps ba ake yawan cewa idan mutum zai ranci kudi ko kuma zaiyi wani amfani dasu za'a bukaci yasa BVN dinsa to magana ta gaskiya yan damfara ta yanar gizo da dama sune ke kirkirar wadannan Apps din da niyyar zasu bada wani tallafi wanda daga zarar mutum yasa BVN dinsa shikenan.
Wannan yasa kamfanin Google da kansa yai wata sanarwa kwanan baya akan cewa zai goge wasu Apps da yawa ko kuma zai daina amfani dasu saboda ya gano ana damfarar mutane ta cikinsu ana daukar bayanansu.
Ko rannan naji an debewa wata mata kudinta bayan ta bada BVN dinta.
To dan haka dan Allah ku guji dora BVN dinku akan Apps din da baku sansu ba sannan ku daina turawa mutane sirrinku.
Comments
Post a Comment