SABON SALO: Ganduje Zai Rabawa Talakawan Kano Akwatunan Talabijin Dubu Ɗari (100,000) Kyauta
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta siyo akwatunan talabijin 100,000 domin siyar wa talakawa kuma ainihin ƴan jihar a farashi mai rahusa.
Gwanduje ya faɗi haka a taron ‘Digital Switch Over’ da aka yi a garin Kano ranar Talata.
“Gwamnati za ta haɗa hannu da kamfanin dake ƙera talabijin din Set-Top-Boxes dake ƙasar nan domin a samar wa talakawa a ƙananan hukumomi 44 a jihar da talabijin din kallo.
“Yanzu gwamnati za ta fara siyo akwatunan talabijin 10,000 inda daga ciki za a bai wa ma’aikatu 700, talabijin 70 a baiwa jami’o’i 15 sannan a raba talabijin 1,460 ga makarantun sakandare da ofisoshin siyasa a jihar.
Ganduje ya ce ya bada odar a siyo talabijin 44,000 domin a raba a kananan hukumomin jihar.
Ya ce za a raba wa kowacce karamar hukuma talabijin guda 1000.
“Za a raba talabijin din ga cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko, makarantun yaki da jahilci, makarantun firamare, ofisoshin kananan hukumomin da wuraren kallo a duka kananan hukumomin jihar.
Ganduje ya ce gwamnati ta horas da wandan za su rika zuwa kananan hukumomin domin hadawa da gyarar talabijin din idan suka lalace.
Shugaban hukumar NBC Balarabe Shehu-IIelah ya ce gwamnatin jihar Kano ta yi lissafin za ta rabawa gidajen talakawa 2,147,005 da gidajen kallo miliyan 1.6 talabijin a jihar.
Shehu-IIelah ya ce gwamnati na tsamanin gidajen mutanen da gidajen kallo za su karu nan da karshen shekaran 2021.
Ya ce sakamakon binciken da NBC ta yi a shekarar 2017 ya nuna cewa mutum 12,882,030 ne ke zama a jihar Kano.
“Shi yasa raba talabijin din ga talakawa ke da mahimmanci a shirin DSO din da gwamnati ke kokarin yi.
A karshe sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado-Bayero ya yaba kokarin fara wannan shiri da gwamnatin tarayya ta yi ganin cewa shirin zai taimaka wajen wayar da kan mutane al’adun kasar nan da sauran kasashen duniya.
Comments
Post a Comment