Kabilar da basa saka kaya
Duniya nada matukar girma kuma nada fadin gaske wannan yasa mutanen dake cikin duniyar ma suke da yawa.
Duk inda aka samu yawa dole a samu abubuwa da yawa, walau kabilu, al'adu da kuma dabi'u masu yawa.
Cikin kabilun dake cikin duniya in za'a bewa mutum labarin kowacce kabila da yadda suke rayuwarsu abin zai bewa mutum mamaki kwarai da gaske.
Wasu kabilun za kaga dabi'ar da suke ko kadan bata dace ba amma su babu ruwansu haka suke gabatar da ita, kamar irinsu kabilar da suke cinye gawar yan uwansu idan sun mutu memakon su binne su, ko kuma kabilar da suke kone matar da mijinta ya rigata mutuwa dadai sauransu.
To yauma cikin shirin namu muna tafe muku ne da labarin wata kabila dake Nigeria wacce su haka kawai suke basa sanya kaya.
Kabilar KOMA wata kabila ce dake zaune a wani yanki na jihar Adamawa dake kasar Nijeriya can cikin karamar hukumar ganye.
Su wannan kabilar har yanzu basu amince da sanya tufafi a jikinsu ba kamar kowa saidai suna yawo tsirara, koda yake wasu suna sanya ganye suna dan rufe wasu guraren a jikinsu.
Sannan wani abin mamaki ga wannan kabilar shine aboki zai iya baiwa abokinsa matarsa ya kwana da ita.
Comments
Post a Comment