Yadda za'a bi a kawo tsaro a hanyar Kaduna zuwa Abuja
Wadannan motocin yaki da kuke gani masu sulke ne wanda harsashin bindiga da RPG baya hudawa, Maigirma Gwamnan jihar Borno ya sayi guda 8 ya bawa 'yan sanda domin su kula da wani gari a Borno wanda yake kan iyakar Nigeria da Chadi
Gwamnan Borno ya sayawa 'yan sanda motocin domin su kare fararen hula daga harin annoba 'yan Boko Haram a kokarinsa da yake na mayar da 'yan gudun hijira zuwa garuruwansu na asali
Idan Gwamnatin jihar Borno zata iya sayan wadannan motoci masu sulke me ya hana Gwamnatin jihar Kaduna da Ma'aikatar kula da babban birnin tarayya Abuja ba zasu sayi irin wadannan motoci guda 100 a bawa 'yan sanda suyi 24hrs patrol akan hanyar Kaduna zuwa Abuja ba?
Ina da tabbaci idan sukayi hakan, har abada ba za'a sake tare wani akan hanyar Kaduna zuwa Abuja ba?, me yasa basuyi ba? ko akwai wani makirci akan hanyar Kaduna zuwa Abuja da aka boye ne?
Muna bukatar e-Security a halin da ake ciki a Nigeria na taba fada a baya, karkashin fasahar dake cikin Electronic Security za'a kirkiri wata irin manhaja kamar application wanda kowa zai iya saukewa akan wayarsa
Abubuwa da za'a saka akan wannan application shine da zaran matafiyi da yake tafiya a cikin mota ya bude application din, zai nuna masa abinda yake gabansa da kuma gefensa, idan akwai mutane suna rike da makami zai nuna, har ma da kala ko samfurin makamin da suke rike dashi zaiyi detecting ya nuna
Kirkiran wannan fasaha zai kawar da batun a tare matafiya a cikin mota a kan hanya a musu fashi ko ayi garkuwa da su, kuma zai taimaki jami'an tsaro su samu cikakken kariya daga fadawa tarkon harin kwanton bauna (ambush)
Masu iko da tsaron Nigeria sun fini sanin wadannan abubuwa da suke cikin ilmin e-Security wanda yake tafiya da cigaban zamani, kuma ba wani kudi mai yawa za'a kashe wajen kirkiran wannan fasaha ba
Yaa Allah duk wani shugaba da ya gaza wajen kawo sauyi a matsalolin tsaron Nigeria ka kawar mana dashi, Ka kawo wanda zasu iya ba don halin mu ba
Comments
Post a Comment