Min menu

Pages

Ƙabilar suke fita yin farauta da MIKIYA

Ƙabilar suke fita yin farauta da  MIKIYA 



Kowacce kabila akwai abinda suka dauka suka rike a matsayin hanyar yin kasuwanci ko sana'a to suma wannan kabilar sun dauki mikiya ne a matsayin makamin da suke farauta ko yin sana'ar da suke samun abubuwa da ita.


Kimanin shekaru masu ɗunbin yawa ne dai Ƙabilar *KAZAKH* suka ɗauka suna Anfani da mikiya gurin farauta kamar yadda wani ɗan kabilar mai suna BIKBOLAT yake faɗamana cewa:


Sudai wannan ƙabila tasu suna kama macen mikiya ce bayan kwanaki da haihuwar ta a cikin sheƙar ta, sannan su koyar da ita tashi da duk wani dubaru irin na farauta, a cewar shi Macen Mikiya tafi Namijin ƙoƙari gurin yin farauta da duk wani iya dubaru na farauta in da Mikiyar tana ɗauke da fuka-fukai masu faɗi kimanin 3m sanan tana da tsawon tsaratan yazo kimanin 6cm in da take iya ɗaukar abu mai nauyi 6kg hakan yasa take kai farmakin ta ga irin su Dilla, da sauran su a yayin da suka fita farauta.


Su dai wannan ƙabilar suna koyar da yaran su dabaru koyar da mikiya yadda zata farauci wani abu tun daga sama, tun yaro na da shekara sha uku 13yrs yake fara fita farauta.

Kamar yadda kuka sanine cewa farauta dai na Maza ne ba Mata ba, to su dai ƙabilar *KAZAKH* Har da yara mata kamar yadda muka ji ta bakin wata ƴar kabilar cewa tun tana da shekara sha uku ta fara fita farauta, domin fita farauta da mikiya al'adansu ce da ta gada daga gurin iyaye da kakanni.

Su dai wannan ƙabila suna matuƙar girmama Mikiya don har ware mata wani lokaci guda sukayi da suke kira da *eagles festival* wato bikin ranar mikiya wadda suke gabatar da shi a babban fadar garin na su mai suna *OLGII*.


Sai dai kimanin shekaru goma kenan da suka wuce al'adar wannan ƙabila Farauta da Mikiya ta fara ja baya, domin yawan cuɗanyar su da wasu mutanen garuruwa, da tura yaransu birane gurin saye da sayarwa.

                  Ga bidiyon a kasa




Comments