Kasashe goma mafiya talauci a Africa
Talauci abu ne da yayiwa kasashen Africa katutu domin an bayyana Africa a matsayin alkarya mafi talauci a fadin duniya baki daya, saidai duk da haka dole akwai kasashen da suke gaba gaba koda a duniya ne wajen arziki a cikin African to saidai kashashen da suke da talauci su suka fi rinjaye da kaso mafi tsoka a cikin nahiyar ta Africa.
Yau cikin shirin namu muna dauke muku ne da jerin wasu kasashe guda goma wanda bincike ya nuna cewa sunfi ko ina talauci a nahiyar African baki daya, wannan yazo ne saboda basa fitar da wasu abubuwa ko kuma basu da albarkatun kasa mai yawa da zaisa sunan kasarsu yayi sama cikin jerin masu arziki daga cikin kasashe.
Koma dai suna fitar da wasu abubuwa kuma koda suna da wasu albarkatun kasa to za kaga yunwa ko kuma wani yanayi yasa wannan kasar ta fito a jerin kasashe mafiya talauci.
Sannan su wadannan kasashen basu da wata babbar cibiya ta kasuwanci da suke shiga da fita tsakanin kasashen Africa dama sauran kasashen Duniya baki daya.
Dan haka ga jerin kasashen da bincike ya nuna sunfi ko ina talauci a nahiyar Africa baki daya.
1 Burundi
2 Somalia
3 Central African republic
4 Congo
5 Niger
6 Mozambique
7 Liberia
8 Malawi
9 Madagascar
10 Chad
Wadannan sune kasashen da aka bayyana sunfi talauci a nahiyar Africa baki daya
Comments
Post a Comment