Min menu

Pages

Matar da tayi shekara 40 batayi bacci ba

 Matar da tayi shekara 40 batayi bacci ba



Abubuwan mamaki da al'ajabi dai basa karewa a duniya, dole idan mutum yana raye zai rika cin karo da labarin wasu abubuwa da za suyi matukar girgiza shi, idan labari aka bashi wasu zai yadda wasu daga cikin labaran kuma bazai yadda dasu ba.


Kwanakin baya mun kawo labarin wani da ya daga hannunsa na dama bai sauke ba har tsawon shekaru 45 mutane sukai ta maganganu suka nuna basu yadda ba ko kadan saida mutane sukai bincike wasu ma suka duba google sannan suka yadda.


To yauma dai muna dauke muku da labarin wata mata yar kasar China mai suna  Li Zhanying da ta zauna har tsawon shekaru 40 ba tare da tayi bacci ba.


Kamar yadda masu ilimi akan jikin dan Adam da kuma yadda sassan jikinsu ke aiki suka ce kowanne Dan Adam ana bukatar ya samu bacci sau daya a cikin awa 24.


To dake duniyar tanada fadi kuma mutanen dake cikin duniyar sunada yawa wannan yasa ake samun mutane masu baiwa kala, a cikinsu ne aka samu Li Zhanying matar da tayi shekaru 40 ba tare da tayi bacci ba.


Wannan abin nata ya bewa duniya mamaki baki daya, domin duk wanda yaji labarin ba karamin kaduwa yake ba.


Kuma manyan likitoci sunyi magana cewar duk wanda bai samu bacci ba na tsawon ranaku to zai iya kamuwa da cuta Amma abin mamaki ita wannan matar babu abinda tayi ko kuma ya same ta.


Mijinta da kuma makotan da suke tare da ita sun tabbatar da cewa wannan matar bata bacci.


Domin mijin yace tunda ya aure ta bai taba gani tayi bacci ba, lokacin da kowa yake kwance ita kuma a lokacin zaka ganta tana zaune tayi shiru ko kuma tana yin wasu aikace aikacen.


Da aka tambayeta yaushe rabonta da tayi bacci sai tace tun tana karama lokacin da bata fi shekaru biyar zuwa shida ba, tun daga wannan lokacin bata sake rintsawa ba, domin ko taso tayi baccin baya zuwa, tun abin yana damunta harta hakura ya daina damunta.






Comments