Wasu kabilu mafiya hatsari a Duniya
Akwai kabilu masu hatsari gaske dake cikin duniya wanda da mutum ya hadu dasu ko yayi arangama dasu kwara yayi gaba da gaba da manyan namun dawa kamar zaki ko damisa saboda yadda suke da bada tsoro da kuma saurin halaka duk wani da ya shiga inda suke ko kuma yayi musu wani abu da basu gamsu dashi ba.
Kalli bidiyon a kasa
Kabilun basu da kyau ko kadan wajen daukar doka a hannunsu ta halaka duk wani da basu saba dashi ba ko kuma ya shiga sabgarsu.
Wasu naman yan uwansu suke ci wasu ma gasawa suke su cinye yayinda wasu jinin suke shanyewa.
Yau cikin shirin namu zamu kawo muku jerin wasu kabilu guda takwas mafiya hatsari a Duniya a cikinsu kuma zamu zabi guda hudu na farko muyi dan bayaninsu.
Dan haka ga jerin kabilun nan wanda bincike ya nuna sunfi hatsari a Duniya baki daya.
1 kabilar yaifo
2 kabilar karowai
3 kabilar Suri
4 Kabilar Yanomami
5 Kabilar Korubo/ Dslala
6 Kabilar Mashco-Piro
7 Kabilar Moken
8 Kabilar Ayoreo
=> Kabilar yaifo ita ce ta daya daga cikin kabilun takwas mafiya hatsari a Duniya domin ko kadan tsarin kabilar batayi ba sannan babu abinda suka fi tsana fiye da bako domin daga zarar bako ya tunkari inda suke tun daga nesa zasu fara sakar masa ruwan kibiya kabila ce dake can zaune cikin a wani guri da yake da suna Papua dake new guinea.
Kabilar Karowai itace ta biyu cikin jerin kabilu takwas masu hatsari a Duniya an bayyana wannan kabilar a matsayin kabilar da suke cinye naman mutane sannan tanada hatsarin gaske, shiga cikinsu ko tunkarar inda suke ga mutumin da bai shirya ba abune mai hatsari.
Kabilar Suri ita ce tazo ta uku cikin kabilun takwas masu hatsari domin tun ganin farko idan kayi musu zaka fuskanci suna da bada tsoro domin za kaga sun tsaga leban bakinsu sunsa wani abu mai kamar warwaro a ciki haduwa da wannan kabilar ga mutumin da bai shirya ba akwai tashin hankali mai ban tsoro suna zaune ne acan wani yanki na kasar Ethiopia.
Kabilar Yanomami Kabilar yanomami wata kabila ce dake zaune can wani yanki mafi nisa a wani layi da ya hada kasar Venezuela da Brazil.
Kabilar yanomami Sun samo asali ne tun can wajen shekarar 1759.
Su dai wannan kabilar kwata kwata basu amince su binne dan uwansu ba idan ya mutu saidai su yanka namansa su gasa su rarraba sannan su cinye.
To jama'a anan zamu dakata mu hade daku a wani sabon shirin.
Comments
Post a Comment