Assalamu alaikum yan uwa barkanmu da wannan lokacin ya kuke ya aiki ya hakurin kasancewa tare damu hakika muna matukar jin dadin yadda kuke kasancewa tare damu a koda yaushe muna godiya sosai da sosai.
Yau cikin shirin namu munzo muku ne da kadan daga cikin tarihin wani gwarzon namiji da akai a Nigeria wanda tarihi bazai taba mantawa dashi ba saboda na mijin kokarin da yayi wa kasar Nijeriya a lokacin da yake raye wato sir Abubakar Tafawa Balewa.
Kamar yadda labari yazo mana dashi an haifi Abubakar Tafawa Balewa a shekarar dubu daya da goma sha biyu a jihar Bauchi dake kasar Nijeriya inda ya fara karatun makarantar firamare a garinsu na Tafawa Balewa bayan ya gama sai kuma ya koma Bauchi middle school.
Daya gama sayya wuce wata makarantar koyon aikin koyarwa a jihar Katsina inda ya karbi shaidar zama malami inda ya koma wannan makarantar daya baro wato middle school ta Bauchi ya fara koyar da dalibai harshen turanci.
Cikin shekara goma Abubakar Tafawa Balewa ya zamto a jerin malamai na farko a shekarar gaba ya samu admission a wata makaranta a London inda yaje yayi diploma a shekarar 1946.
Daga karshe ya dawo wannan makarantar ta middle school dake Bauchi a matsayin headmaster kuma ya zama daga cikin mutane masu kula da makarantun Nigeria a lokacin.
Abubakar Tafawa Balewa ya zama malami mai kwazo kuma yana daya daga cikin mutanen da suka fara zuwa London karatu
Daga nan shi da suka hadu shida yariman sokoto Alhaji Ahmadu Bello suka kafa wata jam'iyya ko kungiya NPC wato Northern People's congress wanda take wakiltar musulmai musamman na arewacin Nigeria baki daya.
An zabe shi a matsayin dan majalisa a tsagin arewa inda a shekarar 1955 aka sake bashi ministan ayyuka da tafiye tafiye a wato a lokacin mulkin turawa kenan lokacin sir James Wilson Robertson.
Bayan an bayyana Nigeria a matsayin kasar da za'a bawa yancin kai gaba kadan sai aka bashi mukamin prime minister, ya tsaya a mukamin prime minister har bayan Nigeria ta samu yancin kai inda sukai aiki shida nmandi Azikiwe wato shugaban kasa na farko a tarihin Nijeriya.
Abubakar Tafawa Balewa yayi aiki tukuru wajen gina hanyoyin tafiye ta ruwa da kuma hanyoyin jirgin kasa da sauran abubuwa.
A takaice dai tun shekarar 1952 zuwa mutuwarsa Tafawa Balewa ya rike mukamai masu yawa wanda yai amfani da damarsa wajen yiwa kasar hidima sosai.
Daga karshe dai an kashe shi tare da jefar da gawarsa bayan wasu abubuwa sun faru a shekarar 1966.
Mu kasance tare daku a wani sabon shirin.
Comments
Post a Comment