YADDA A KE KUNNOWA MACE NAGUDA
INDUCTION OF LABOR
Wanan wata hayace da a ke sanya mace ta ke fara naquda ta sanadiyyar amfani da Magani ko kuma abun aiki domin a samu mace ta haihu ba tare da an yi mata aiki ba.
Ana sanya mace ta fara naquda ne idan har ya zamanto akwai dalilai da za su iya haifar da matsala ta bangaren uwa ko kuma bangaren jariri. Wani lokacinma a na duba maslahar uwar ne domin ba ta kariya daga wasu matsaloli wannan ya sa hadafinmu anan ya fi karkata bangaren uwa.
DALILAN DA YA KE SAWA AYI
DALILAI NA BANGAREN JARIRIN DA KE CIKI:-
*mutuwar jariri a ciki
*Cikin da ya wuce sati 41
*Yan biyu Wanda su ka huce sati 38
*Daina girman yaro a ciki
*Qarancin ruwan da yaro ya ke Rayuwa aciki da sauransu.
DALILAI NA BANGAREN UWA :-
*matsanancin hawan jini
* hawan jini wanda juna biyu ya haifar da shi
*jijjiga
*Fashewar member
*Ciwon sugar tare da Cikin da ya wuce sati 38
*Ciwon sanyi na mata
Da sauransu
ABUBUWAN DA SU KE HANAWA AYI
*duk wani dalili da zai sa mace ba za ta haihu da kanta ba Sai dai a yi mata aiki (CS)
(Misali)
* sakkowar mahaifa ta rufe OS ( placenta previa)
*sakkowar jijiyar yaro ta rufe Os
( vasa previa)
*Zaman yaro ba daidaiba
*wadda aka tabayiwa aiki
* wadda aka sameta tana dauke Da cuta bayan An yi CERVICAL SMEAR
*Yanayin Qudu ya zama ba na mataba
*Cikin qasa da sati 35
*Bugawar zuciyar yaro yazama ba daidaiba.
*in yazama bishop’s score qasa da 6 , wannan dole sai anyimata cervical ripening kafin induction.
Wannan sune dalilai dake hana a sanya mace tafara naquda
HADARIN DA SU KE HAIFARWA
* Ya na haifar da motsin yaro yayi yawa
*Ya na haifar da fashewar uterus
*ya na haifar da Fetar Distress
*ya na sanyawa a Haihu kafin lokaci
*ya na haifar da sanadiyyar da wasu qarshe sai an yi musu aiki.
Ya Allah Ka sauki masu dauke da juna 2 lafiya masu nema Allah Ka basu masu albarka
Abin sadaqa ayiwa Annabi Sallallahu Alaihi wasallam Salati
Comments
Post a Comment