Min menu

Pages

Za kayi dana sani matukar baka koyar da yayanka wannan abubuwa 7 din ba

 Za kayi dana sani matukar baka koyar da yayanka wannan abubuwa 7 din ba




Yaya wata kyauta ce da Allah madaukakin sarki ke yiwa bayinsa maza da mata, amma wani lokacin muna sakaci ko barin yaranmu su shiga wani hali ko yana yi wanda baya yin tunanin cewar wannan yayan fa kyautar Allah ce daya bamu.

Bama lura da cewar wasu ma sunyi bakin kokarin su domin su samu amma Allah bai basu ba, bawai dan baya sonsu bane ko kuma yafi sonmu ne w kansu ba.

To yau cikin shirin namu zamu kawo muku wani bayani ko kuma zamu zayyano muku wasu abubuwa guda bakwai da za muyi matukar dana sani ko kuma muyi kuka da idanunmu matukar bamu koyawa yayanmu wadannan abubuwan guda bakwai din ba.


Su zama masu gaskiya:- Duk lokacin da ka haifi yara to yana da kyau ka dage ka ga sun zama masu gaskiya karka yadda su taso a matsayin marasa gaskiya, duk lokacinda baka koyar da yaranka cewar su zamto masu gaskiya ba to gaskiya zakayi kuka da idanunka koda gaba ne.


Koyar dasu yadda za suyi magana da mutane:- A shawarce duk lokacinda ka haifi yara to yana da kyau ka koyar dasu yadda za suyi magana da mutane wajen saukaka murya da kuma girmama maganganun da mutane ke musu.

Duk lokacinda baka koyar da yaranka magana mai kyau ba to zaka iya yin kuka da idanunka wata rana.

Girmama mutane:- Duk rintsi ka koyar da yayanka girmama mutane da kuma yawan gaisuwa duk lokacinda suka ga mutanen da suka girme su.


Koyar dasu tarbiyya:- Koyar dasu tarbiyya na daya daga cikin abubuwan da ake so mutum yayiwa yayansa domin yanada mahimmanci sosai.


Basu ilimi:- Kayi duk yadda za kayi ganin yaranka sunyi karatu domin rashin yin karatu a gunsu kan zamto wata mummunar hanya ta tabarbarewar komai nasu wanda idan suka tabarbare kaima abin zai shafe ka sosai.

Da haka dan gudun yin kuka da idanunka gaba kayi bakin kokarin ka wajen basu ilimi.


Hana su yin mu'amula da mutanen banza:- Duk lokacin da yayanka suka fara tasawa ya zama sun fara magana ko sanin mutane to kana gargadarsu akan koda wasa kaga ka gansu suna mu'amula da mutane masu halayya kaza saika fada musu duk irin halin banzar da baka so suna aikatawa ko yin mu'amula da masu wannan halin.

Idan baka hane su ba to a karshe kaine za kayi kuka da idanunka.


Ka hana su son kayan wani ko tambayar wani kayansa:- Duk lokacinda ka haifi yara to kayi kokari wajen hana su tambayar kayan wani ko rokon mutane abu kamar kudi da sauransu domin duk lokacinda baka hane su aikata irin wadannan abubuwan ba akwai matsala koda gaba.


Wadannan sune kadan daga cikin abubuwan muna fatan kunji dadinsu.

Comments