Ƙasashe goma da suka maida karuwanci babbar sana'a
Karuwanci dadaddiyar sana'a ce da wasu ƙasashe suka riƙe ta da matukar muhimmanci wanda wasu suke ci kuma su sha daga gareta.
Wannan yasa mukai bincike muka zakulo muku wasu daga cikin kasashen da suka rike sana'ar karuwanci da mahimmanci harma suka mayar da karuwancin sana'ar su.
Ga jerin sunayen ƙasashen nan.
1.FINLAND
Ƙasa ce da tayi fice gurin karuwanci, in da basu ɗauki zina a bakin komai ba, in da a fili ma zakuga sunayi.
2.COSTA RICA
Ita ma ƙasa ce da suke da yawan gidajen karuwai, da ƴan daudu masu zaman kansu, sun ɗauki karuwanci sana'a mafi muhimmanci.
3.NEW ZEALAND
Tana daga cikin ƙasashen da gwamnatin su ta yardar da fara karuwanci a shekara ta dubu biyu da uku, in da suka zartar da fara karuwanci a bisa dokoki da tsarin masu kiwon lafiya don tabbatar da suna gudanar da sana'ar ta su haɗi da kiyaye lafiyan su.
4.AUSTRIA
Su kuma akwai rijista na mussamman da mace zatayi kafin ta fara karuwanci, kuma sai an gabatar mata da test an tabbatar da lafiyan ta ƙalau, sannan akwai harajin da zasu dunga biya.
5.BANGLADASH
Kowa ta irin harka da ya danganci neman mata da sauran su, an halasta yin shi a ƙasar amma ban da neman maza.
6.DENMARK
Shima ƙasa ce da suke harkan karuwanci, ko police bai da izinin kama karuwa a ƙasar saboda gwamnati ta san da zaman su.
7.CANADA
Babu wata doka a ƙasar da ta hana yin zina don neman kuɗi, kuma akwai yawaitar gidajen kkaruwai masu zaman kansu.
8.GERMANY
Suna da kimanin karuwai dubu ɗari huɗu, sannan duk wata karuwa tana pension ɗinta a hannun gwamnati matuƙar tayi rigerster, sannan suna da insuran lafiya, sanan suna aiki 40hour.
9.GREECE
suma zakiyi karuwancin ki matuƙar ba tilasta ki akayi ba sannnan zakiyi medical card wanda zaki dunga sabanta shi duk bayan sati biyu.
10.COLOMBIA
Suma ƙasa ce da suka yarda da karuwanci a matsayin sana'a.
Comments
Post a Comment