Min menu

Pages

Kasa daya tilo a Afirka da ba a gudanar da zabe ba tun bayan samun 'yancin kai.

Kasa daya tilo a Afirka da ba a gudanar da zabe ba tun bayan samun 'yancin kai.



Haƙiƙa a duk lokacin da wata ƙasa ta samu yancin daga turawan mulkin mallaka, to ana sa mata ran samun sauƙi da salama. Amma zai zama abin mamaki idan aka fahimci cewa mutanen da suka yi gwagwarmayar neman ‘yancin kai su ne suke zaluntar 'yan ƙasar tasu.  Akwai ƙasashe da yawa a Afirka waɗanda ke aiwatar da mulkin demokraɗiyya, sai ƙasar da muke labari akanta wato Eritrea ba ta cikin su.  Duk da cewa suna da jam’iyyar siyasa, amma su kadai ne ke kan mulki tun daga shekarar 1991.


 Ga wadanda ba su san ko wane ne shugaban kasar Eritiriya ba, sunansa Isaias Afwerki, ya jagoranci mayakan 'yantar da jama'ar Eritiriya zuwa nasara a kan ƙasar Habasha a shekara ta 1991. Tun bayan zabensa da majalisar dokokin kasar ta yi a shekarar 1993, a zabukan gama gari da aka gudanar tun wancan lokacin.  

 Shugaban kasar yana da ƙarfin iko a majalisa a  zartaswa, wanda hakan ya sa ba za a iya tsige shi ko kiran wani zabe ba dole sai da izinin sa.  Ba zai zo da mamaki ba idan aka fahimci cewa kasar ba ta da tsarin shari'a mai zaman kansa, duk ya rataya ne a kan Shugaban kasa.  Majalisar Dinkin Duniya da sauran kasashe sun yi Allah wadai da matakin, inda suka bayyana kasar a matsayin daya daga cikin kasashen da suka fi danniya a duniya.

 Rahoton ya bayyana cewa kasar ta rufe dukkanin kafafen yada labarai masu zaman kansu da za su iya kalubalantar ikon shugaban kasar, tare da kulle duk wani nau'i na adawa da zai iya adawa da mulkinsa.  Shugaban ya kewaye kansa da wasu ƴan sa-kai da wasu masu yi masa biyayya, suna aiki da umarninsa.

 Shugaban Eritrea mutum ne mara tausayi, yana murkushe 'yan adawar sa ba tare da nadama ba.  Mutane da yawa sun zarge shi da mulkin kama-karya, inda suka yi tir da shi bisa laifuka da dama na cin zarafin dan Adam.  Don haka da yawa daga cikin ‘yan kasar na yin kasada da rayukansu don gudun hijira daga wannan kasa zuwa Gabas ta Tsakiya ko kuma Turai.

 Tsakanin Eritriya da Koriya ta Arewa, ban san wace ƙasa ce ta fi muni ba.

Comments