Wasu alamomi guda uku da mace zata gane ta dauki ciki har yayi sati biyu.
Wani lokacin wasu matan basu iya gane sunada ciki tun a farko musamman wadanda suke sabin ma'aurata ne, kuma basu taba yin ciki ba.
Wasu ma gane suna da ciki har sai sunje asibiti an gwadasu sannan ake sanar dasu cewar suna da ciki har na adadin lokaci kaza.
To yau zamu bayyana muku wasu alamomi guda uku da idan mace ta samu karuwa zata gane koda a farkon sati biyu ne da samun karuwar tata, wannan zaisa mace ta fara tanadi kuma ta fara cin abinci mai gina jiki da kara lafiya wanda jaririn dake cikin ta ma zai kara lafiya idan ya girma, sannan ta guji amfani da wasu abubuwa ko magunguna da kan iya sawa cikin ya zube.
1. Tashin zuciya da kuma amai:- Duk matar da ta samu karuwa ba'a rasata da wadannan abubuwan guda biyu tashin zuciya da kuma amai, kodai bata amai to kuwa zuciyarta zata rika tashi tana jin kamar za tayi amai.
Daga zarar mace tayi aure ta fara jin wadannan alamomin to ta samu karuwa kenan Dan haka muna tayata murna.
2. Girman mama da cikowarsu:- Haka kawai idan ciki ya shige ki zaki ga mamanki suna kara girma kuma sun cicciko saboda akwai hormones din da suke aiki kuma sai mace ta samu juna suke gabatar da sauran aikace aikacensu, Dan haka koda babu alamomin da muka ambata a sama amma sai aka samu wannan to mace na dauke da ciki.
3. Daukewar al'ada:- Daga kinga al'adarki ta dauke ko kuma baki ga al'adarki ba lokacin da kika saba ganinta to alamu ne na cewar kina da ciki.
Wadannan sune kadan daga cikin alamomin da mace zata gane ta dauki ciki.
Comments
Post a Comment