Min menu

Pages

Wasu manyan kasuwanni mafiya girma da shahara a Nahiyar Africa

 Wasu manyan kasuwanni mafiya girma da shahara a Nahiyar Africa



Africa yanki ne babba wanda ya tara abubuwa mafiya yawa na birgewa tare da kawatarwa wanda yasa har mutane daga wata uwa duniya kan shigowa domin gabatar da abubuwan su, daga cikin abubuwan da Africa take dashi mafiya shahara tun a karni mai tsawo da ya shude harda kasuwanci.


Harkar kasuwanci wata harka ce da ta dade a Africa tun tsawon lokaci, wanda ta dalilin harkar kasuwancin ne wasu da yawa sukai kudi, wanda ake bada labarinsu tun daga manyan sarakunan da suka shude har zuwa yanzu.


Akwai hanyoyin kasuwanci sosai a Africa ana gabatarwa kama daga nau'ikan kaya na nomawa da nayin harkokin yau da gobe.


Yau cikin shirin namu zamu kawo muku jerin wasu manyan kasuwanni da sukai fice a Africa wanda ake gabatar da kasuwa Mai ban mamaki, Dan haka muje cikin shirin.


Khan El Khalid;- Wannan wata babbar kasuwa ce dake birnin Cairo dake kasar Egypt wato masar, wannan kasuwar tana daga cikin manyan kasuwanni a Africa baki daya, an bude ta tun a karni na goma sha hudu.

Ana sayar da kayayyaki masu yawa a wannan kasuwar.


Onisha;- Kasuwar Onisha kasuwa ce data kasance babba kuma take ci kusan kowacce rana Banda ranar lahadi, kasuwa ce dake kasar Nijeriya.


Duk wanda suke ziyartar wannan babbar kasuwar ta garin Onisha zai fadi yadda take, ana sayar da kaya kala daban-daban kuma na yau da kullum.


Kejetia:- Kejetia kasuwa ce da take garin kumasi na kasar Ghana kasuwa ce mai matukar girma da kyau tare da tsaruwa, ana sayar da kaya kowanne iri da ake bukata na yau da kullum.

Fes Medina:- Fes medina kasuwa ce da take fes a kasar Morocco kusan kasuwa ce da ake sayar da abinci na daga dangin abubuwa na yau da kullum, kasuwa ce tsohuwa wacce ta wanzu tun a karni na Tara.

Maasai:- Kasuwar Maasai kasuwa ce dake cikin Nairobi ta kasar kenya wacce ake budeta daga ranar asabat zuwa ranar alhamis, kasuwa ce babba da ake sayar da kayayyaki masu yawa, ku ziyarci kasuwar kusha kallo.


Owino:- Kasuwar Owino ta kasance kasuwa guda kuma mai matukar kyau da girma da akayi mata bangarori a cikinta, kasuwa ce dake birnin kamfala a kasar Uganda. Kowa ya ziyarci wannan kasuwar zai bada labari na yadda take a tsare tare da yawan kayayyaki.


Addis markato :- Kasuwar Addis markato ta zamto daga cikin kasuwanni mafiya shahara kuma babba a nahiyar Africa wacce take birnin Addis Ababa na kasar Ethiopia.


Babbar kasuwa ce da take ci sosai kuma tana da girma sosai.


Anan zamu dakata 

Comments