Min menu

Pages

Wasu tsofin jami'oi 4 a Duniya wanda a Africa suke 1 daga ciki ma mace ce ta gina ta.

 Wasu tsofin jami'oi 4 a  Duniya wanda a Africa suke 1 daga ciki ma  mace ce ta gina ta.



Mutane da yawa sukanyi tunanin duk wasu jami'oi mafiya dadewa ko kuma mafiya shahara a nahiyar turai kawai suke to amma ba haka bane, a nahiyar Africa ma akwai wasu manyan jami'oi wanda suka dade kuma daya daga cikinsu ma mace ce ta gina ta.


Dan haka yanzu kai tsaye zamu tafi cikin bayanan wadannan jami'oin tare da kawo sunayensu.

Ez-Zitouna university:- Jami'ar Ez zitouna Jami'a ce dake kasar Tunisia makaranta ce da ta jima sosai a duniya domin an ginata ne tun shekaru masu matukar yawa da suka shude.

Makaranta ce da ake koyar da abubuwa da dama da suka shafi bangaren kimiyya da kuma sauran abubuwa.


Alqarawiyyin University:- Jami'ar Alqarawiyyin makaranta ce dake kasar Morocco wanda itama tsohuwar Jami'a ce da aka ginata tun shekaru masu yawa da suka gabata domin an ginata ne tun 859 AD wanda wannan Jami'ar mace ce ta gina ta mai suna Fatima alfihri, wanda tayi amfani da dukiyar mahaifinta ta gina masallacin Alqarawiyyin wanda ake koyarwa a ciki inda daga karshe ya koma Jami'a.


Al-Azhar University:- Jami'ar Al'azhar makaranta ce ta uku a tsufa tun kafuwar wadannan biyun da muka bayyana a baya, Jami'a ce dake kasar masar wato Egypt wanda aka kafata tun a shekarar 970 AD. Makaranta ce babba wacce take tara mutane daga ko ina a fadin duniya, domin ance duk shekara tana daukar dalibai a kalla dubu talatin.


Sankore University:- Jami'ar Sankore Jami'a ce data samo daga masallacin Sankore domin da masallaci ne wanda daga karshe aka maida gurin Jami'a tare da masallaci.

Jami'ar ta jima sosai domin an kafata ne tun shekaru masu yawa da suka wuce, tun zamanin sarki mansa musa daya daga cikin mutane mafiya arziki a tarihin duniya baki daya, ance wannan sarkin shine ya gina gurin.

To jama'a wadannan sune manyan jami'oin da suka jima a nahiyar Africa baki daya kuma har yanzu suna nan ana kuma bada ilimi a cikinsu. Dan haka anan zamu dakata mu hadu daku a wani sabon shirin.

Comments