Ƙabilu 5 da sukafi ko wace ƙabila dadewa a Nahiyar Afirka
1. Kabilar San
Kabilar San, ana kiran ƴan wannan ƙabila da Bushmen, suna daga kudancin Afirka ne, waɗanda aka fi sani da Khoekhoe.
Anfi samun su a yankunan Botswana, Namibiya, da kudu maso gabashin Angola. Ƙabilar San dai mafarauta ne, kuma sun shafe aƙalla shekaru 30,000 suna zaune a kudancin Afirka kuma an yi imanin ba wai kawai mafi tsufan ƙabilar Afirka ba ce, amma maiyuwa ne mafi tsufa jinsi ne a duniya.
Kasancewar tarihin San a Botswana ya bayyana musamman a yankin Tsodilo Tudun Botswana. Kabilar kuma tana da mafi bambance-bambancen DNA fiye da kowane rukunin 'yan asalin Afirka.
Wannan yana nufin San su ne zuriyar da kai tsaye za a iya cewa sune ƴan adam na asali na a Afrika.
Yadda zaku hana a ganku online a Facebook
2. Ƙabilar Maasai
Kabilar Maasai wata ƙabila ce ta asali da ke zaune a Afirka na ƴan ƙabilar dai makiyaya ne kuma suna zaune ne a Kenya da arewacin Tanzaniya.
Kabilar ta fito ne daga arewacin tafkin Turkana a kogin Nil. Sun fara ƙaura zuwa kudu a ƙarni na goma sha biyar, amma an yi imanin cewa ƙabilar ta wanzu fiye da shekaru dubu uku da suka wuce.
3. kabilar Nama
A cikin ƙabila mafi tsufa a Afirka, ƙabilar Nama ita ce ta 3 a wannan jerin. Suna zaune ne Afirka ta Kudu, Namibiya da Botswana. A al'adance suna magana da yaren Nama na dangin harshen Khoe-Kwadi, kodayake yawancin Nama suna jin Afirkaans.
Kabilar ita ce zuriyar Khoikhoi ta ƙarshe, waɗanda ke da alaƙa da San.
Ƙabilar Nama dai makiyaya ne (masu kiwon shanu), al'adar da ta samo asali ne lokacin da wasu mutanen San suka basu kiwo fiye da shekaru 2,300 da suka wuce.
4. Ƙabilar Berber
Kabilar Berber ’yan asalin Arewacin Afirka ne, musamman Maroco, Aljeriya, Tunisiya, da Libya, da kuma wasu yankuna na Mauritania, arewacin Mali, da arewacin Nijar.
Akwai masu cewa Berbers sun wanzu a yankin Maghreb na Afirka tun lokacin da aka fara rubuta tarihin yankin.
An yi imanin cewa Berbers na wannan zamani su ne zuriyar mutanen sun riga Larabawa mazauna Arewacin Afirka bayyana. Ana ɗaukar ƙabila ɗaya daga cikin tsofaffin ƙabilu a Afirka, ɗaya daga cikin rukunin farko na Berbers sune Caspians, waɗanda suka rayu a yankin sama da shekaru 10,000 da suka gabata lokacin zamanin Neolithic.
5. Ƙabilar Sandawe
Kabilar Sandawe 'yan asalin yankin Kudu maso Gabashin Afirka ne, suna zaune ne a gundumar Chemba na yankin Dodoma a tsakiyar Tanzaniya.
Ana ganin cewa suna ɗaya daga cikin tsofaffin ƙabilu a Afirka, Sandawe sun samo asali ne daga wasu mutane na farko kuma sun yi tarayya da kabilar San, waɗanda aka yi imanin su ne mafi tsufa a nahiyar Afirka ɗin.
Comments
Post a Comment