Ƙasashe 12 a Nahiyar Africa masu arzikin albarkatun kasa amma kuma har yanzu matalauta ne.
An bayyana Nahiyar Africa a matsayin babbar kasa wanda keda matukar girma kuma mai dauke da tarin mutane masu kabila daban daban, wanda suke zaune cikin Nahiyar.
Wasu na zama a gari wasu a kauyuka wasu kuma cikin manyan birane, Nahiyar Africa tayi kaurin suna a bangarori da yawa daga ciki harda albarkatun kasa wanda ake ji dasu a duniya baki daya. Akwai gurin noma gurin kiwo akwai arzikin karkashin kasa kamar su gwala gwalai man fetur, tagulla da lu'u lu'u jauhari da sauransu, haka kuma akwai bishiyoyi wanda suke fitar da yayan itatuwa wanda ake sayarwa masu matukar kudi.
Wannan yasa sunan Africa ya zamto daga cikin kasashe masu albarkatu a bangarori da yawa wanda kusan duk duniya ba lalle bane a samu wani yanki ko kuma alkarya da suke da irin wadannan albarkatun ba.
Saidai duk da wadannan albarkatun da Nahiyar take dashi akwai wasu kasashen a cikin African wanda sune ke kan gaba wajen duk wadannan nau'ikan arzikin to amma kuma matalauta ne, yan kasar dake zaune cikin kasar sunfi yan kowacce kasa talauci da shiga kunci, sune wanda zamu zayyano muku jerin su.
1. Nigeria
Kasar Nigeria itace kasar farko wanda take da albarkatun kasa masu yawa tun daga man fetur da sauran abubuwa amma ita ce kan gaba a talauci a yanzu domin yan kasar kullum kuka suke.
2 Botswana
Kasar Bostwana itama kasa ce da take da karfin albarkatun kasa irinsu diamond Gold da sauransu amma dai talakar kasa ce.
3 South Africa
South Africa tana cikin kasashen masu tarin albarkatun kasa a cikin nahiyar Africa domin suna da albarkatu irinsu chromium, manganese, platinum da sauransu, amma har yanzu kasar na cikin jerin kasashe matalauta.
4. Namibia itama wannan kasar tana daga cikin kasashen masu arzikin albarkatun kasa amma a haka matalauciyar kasa ce.
5. Mozambique
6. Zambia
7. Niger
8. Zimbabwe
9. Egypt
10. Ghana
11. Libya
12. Cameroon
Comments
Post a Comment