Jerin kasashen goma mafiya karfin rundur soja a Duniya baki daya
Kamar yadda kuka sani rundunar soja wata aba ce da kasa ke alfari dashi domin yana sanyawa kasa tayi suna kuma ta daukaka a jerin sauran kasashe kuma ta bada tsoro da shakka ga sauran kasashen da suke son tunkararta da yaki ko kuma yin fada da ita.
Duk kasar da take da rundunar soja mai karfi ba kasafai za kuga wata kasar ta tunkareta da yaki ko kuma neman rigima ba domin ta sani koda an gwabza to da wuya ta samu nasara.
Haka zalika irin kasashen da suke da rundunar soja mai karfi za kuga suna yawan danne wasu kasashen da suka san basu da rundunar soja mai karfi.
Yau cikin shirin namu zamu zayyano muku jerin wasu kasashe masu rundunar soja mafiya karfi a Duniya kuma suke da karfi ko cika ido a kan sauran kasashe, dan haka muje ga jerin sunan kasashen.
1. United States
2. Russia
3. China
4. India
5. Japan
6. South Korea
7. France
8. United Kingdom
9. Pakistan
10. Brazil
Wadannan sune jerin kasashen da suke da karfin soja duk da wasu daga cikin kasashen basu da makamin nuclear amma dai rundunar sojan da suke da ita tana da karfi sosai wannan ne yasa ma suka zamto daga cikin kasashen da suka fi ko ina karfin soja a Duniya baki daya
Comments
Post a Comment