Jerin Wasu Kasashen Duniya Da Suka Canja Sunansu Na Asali.
Wani lokaci kasashen duniya na iya canza sunayensu na asali saboda wasu dalilai na ƙashin kansu. Wasu daga cikin irin waɗannan dalilai sun haɗa da raba iyaka, yaƙi, rarrabuwar kawuna, samun ƴancin kai da dai sauran su.
A ƙasa akwai jerin ƙasashen da suka canza suna na asali zuwa wani daban.
1.) Jamhuriyar Czech: Ko da yake ƙasar ba ta son kawar da Jamhuriyar Czech gaba ɗaya, amman ƙasar tana son a san da ita da Czechia akwai bambancin. Don sauƙaƙa ƙungiyoyin wasanni da kamfanoni don amfani da sunansu akan samfuran su.
Kasar za ta ci gaba da amfani da sunan Jamhuriyar Czech, amma kuma sunan Czechia na nan a matsayin gajeriyar hanya ta faɗar sunan ƙasar.
2.) Kudancin Rhodesia (Southern Rhodesia): A Ƙarƙashin mulkin mallaka, an haɗa kudanci da arewacin Rhodesia a matsayin ƙasa ɗaya. Sai dai bayan samun ‘yancin kai a watan Afrilun 1980, kasar ta sauya suna a hukumance zuwa Zimbabwe.
3.) Swaziland: A shekara ta 2018, Sarkin Swaziland ya canza sunan kasar zuwa Eswatini. Sunan bai zo wa 'yan kasar da mamaki ba, domin a cewar yaren kasar Eswatini na nufin kasar Swaziland ko kuma kasar Swazis.
Saboda haka, tun lokacin, ana kiran ƙasar Afirka da sunan Eswatini.
4.) Jamhuriyyar Macedonia (The Republic Of Macedonia): Bayan kasancewarta na NATO, don bambanta kanta da Masedoniya na Girka, jamhuriyar Macedonia ta yanke shawarar kiran kanta da Jamhuriyar Arewacin Macedonia a watan Fabrairun 2019, kuma ba su canza Macedonia ta ainihi ba.
5.) Ceylon: Ƙasar da Turawan Portugal suka gano a shekara ta 1505 kuma aka fi sani da Ceilao daga baya gwamnatin Birtaniya ta canza su zuwa Ceylon. Duk da haka, bayan samun 'yancin kai, ƙasar ta canza suna zuwa Sri Lanka.
6.) Irish Free State: Bayan da kasar ta yi yaki aka zubar da jini tare da Ƙasar Ingila na shekaru 2, ƙasar ta yanke shawarar cire duk wata dangantaka da gwamnatin Birtaniya, kuma a cikin 1937, hakan yasa ƙasar ta yanke shawarar canza wa ƙasar suna inda ta tashi daga Irish Free State zuwa Ireland.
7.) Burma: Kasar dai da farko ana kiranta da Burma, sai dai hakuntan ƙasar sun sauya mata suna zuwa Myanmar a shekarar 1989, kuma hakan ya biyo bayan yakin da aka yi na murkushe tashe-tashen hankula a kasar.
Majalisar Dinkin Duniya da wasu kasashe irin su Faransa (France) da Japan sun amince da sabon sunan, yayin da Birtaniya (England) da Amurka ba su amince da shi ba.
8.) Farisa: Kasar Iran da ake kiranta da Farisa kafin shekara ta 1935. Sai dai a shekarar 1935 kasar Farisa ta yi kira ga dukkan kawayenta da su rika kiran kasar Iran da sunan kasar ta Farisa. Tun daga wannan lokacin ake kiran kasar da Iran.
9.) Siam: Wannan ƙasa tana daya daga cikin kasashen duniya da ba a taba yi wa mulkin mallaka ba walau daga turawan Birtaniya ko Faransa ba. Da farko dai ana kiran kasar da sunan Siam kuma kasar ta ƙarƙashin mulkin cikakken sarki ne, amma lokacin da ta fara aiki da tsarin mulkin kasar a shekarar 1939, kasar ta sauya suna zuwa Prathet Thai (Thailand), wanda ke nufin ‘yantacciyar ƙasa.
Comments
Post a Comment