Jerin wasu Kudade mafiya daraja a Duniya baki daya
Barka da shigowa wannan gidan, gidan da ake kawo bayanai da suka shafi Duniya da abubuwan cikinta baki daya, kama daga kan mutane, halittun ruwa, na tudu da kuma na gangare.
Gidan da yake kawo labarin kasashe, kabilu da kuma birane tare da bayani akan manyan mutane da suka rayu a zamanin baya da kuma yanzu, sannan yake kawo jerin bayanai akan abubuwan mamaki da dai sauransu.
Yau wannan gidan zaiyi bayani ne akan wasu takardun kudade wanda suka fi daraja a Duniya baki daya, wanda duk wani kudi na kowacce kasar a bayansu yake dan haka muje cikin shirin.
1. British Pound (Pound Sterling) Pound Sterling shine wanda aka fi saninsa da British Pound, an bayyana wannan kudin a matsayin kudi na farko da yafi kowanne kudi daraja a Duniya.
2. Euro shine kudin da yazo na biyu a daraja domin daga British Pound sai shi.
3. United State dollar Duk da sunan da dollar amurka tayi amma bata zamto ta daya ko ta biyu ba a Duniya ita ce a mataki na uku cikin jerin kudade mafiya daraja a Duniya baki daya, amma duk da haka dollar daya daidai take da kudin Nigeria 570 a black market.
Wadannan sune jerin kudade guda uku da muka kawo mafiya daraja a Duniya, duk sauran kudaden darajar su bata kai ta wadannan da muka zayyano ba.
Comments
Post a Comment