Kasashe biyar masu matukar arahar man fetur a Nahiyar Africa
Yau zamu kawo muku kasashe 5 na Afirka da ke da mafi ƙarancin farashin man fetur
Farashin man fetur ya bambanta a kasashen Afirka daban-daban. Wadannan farashin galibi yana shafar abubuwa da yawa. Wasu daga cikin waɗannan abubuwan sun haɗar da haraji, tallafi, hukuma, da wasu muhimman abubuwa na yau da kullum.
Sai dai a wannan makala, za mu duba kasashen Afirka da ke da farashin mai mafi arha a Afirka. Wasu daga cikin wadannan kasashe masu arzikin man fetur ne, kuma a cewar Statistics Times, wannan lamari yakan haifar da karancin farashin man fetur a wadannan kasashe.
1. Libya.
Libya ita ce kasa mafi arha man fetur a Afirka. Alkalumman kididdiga sun nuna cewa Libya na sayar da litar man fetur din ta kan dala 0.03 wanda ya kai kusan naira 13 a kowace lita. Libya kasa ce mai arzikin mai a Afirka!
2. Aljeriya.
Ta biyu a jerin ƙasashen ita ce Algeria. Ana sayar da man fetur din kasar kan dala 0.32 a kowace lita wanda ya kai kusan naira 133 a kowace lita. Wannan a cewar Statistics Times.
3. Angola.
Angola ita ce kasa ta uku a wannan jerin. Wannan kasa ta na sayar da man fetur din ta kan dala 0.34 kan kowace lita, kamar yadda kididdiga Times ta bayyana. Wanda ya yi daidai da Naira 141 a kowace lita.
4. Najeriya.
Ƙasar Nigeria ita ce ƙasa ta 4 a wannan jadawalin kasar da ake mata kirari da Uwar Afrika. Ita ma tana sayar da man fetur mafi arha a Afirka. A cewar kididdiga Times, Najeriya na sayar da man ta akan dala 0.40 kan kowace lita. Wanda ya yi daidai da kusan Naira 164 a gidan man gwamnati a kowace lita, duk da yanzu man fetur din yana Dan wuya a kasar sakamakon wasu abubuwa da suka faru Dan haka wani gurin yana da yar tsada idan har ba'a gidan man gwamnati bane.
5. Misra.
Masar ce kasa ta karshe a jerinmu kasashen da zamu ambato. Kasar dai tana sayar da man fetur dinta kan dala 0.60 kan kowace lita. A cewar Statistics Times, wannan yayi daidai da naira 248 akan kowace lita.
Comments
Post a Comment