Tarihin Ɗan Najariya Da Ya Zagaye Kasashe 87 A Babur – Olabisi Ajala
Mashood Adisa Ajala, mutum ne mai dumbin tarihi cike da burgewa da ban sha’awa.
Shine mutumin da ya zagaye kasashe 87 na turawa a babur inda yayi suna, kuma ya samu daukaka.
Ya kai kololuwa a rayuwarsa, sai dai daga baya ya mutu cikin mawuyacin hali, har iyalansa suka guje shi.
An haifi Mashood Adisa Ajala a Ghana, shekarar 1930.Yana da ƙannai da yayu 24, mahaifinsa yana da mata 4. Bayan haihuwar Ajala, iyayensa suka koma Najeriya, inda yayi karatunsa a Baptist Academy da ke Legas da Ibadan Boys’ High School.
Bayan Olabisi ya kai shekaru 18 da haihuwa, ya tafi jami’ar Chicago, don yayi karatun likitanci. Yana da burin zama likita don ya koma Najeriya ya taimaki mutane, inda bokaye da masu magungunan gargajiya suka fi kamari.
Bayan nan sha’awar tukin keken tsere ta shiga ransa, inda ya fara tseren a shekarar 1952, lokacin yana da shekaru 22 a duniya. A tseren yana yawon 2,280 miles a keke.
Lokacin da ya isa Amurka, yana da burin nuna musu cewa bakaken fata ba sa yawo tsirara ko kuma amfani da fatun dabbobi. Duk inda yaje, yana sanya sutturu irin na gargajiya.
Nan da nan labarai suka fara yawo a kan wani dan Afirika da ke yawo da sutturun gargajiya a keke, nan da nan Ajala ya zama sananne a wannan lokaci.
Har a gidan talabijin da jaridu ake wallafa hotunansa da labaransa, inda ake kwatanta shi a matsayin mutum mai kwarjini.
Bayan nan ne yayi digiri a Psychology a jami’ar Columbia, Ajala ya tara ilimi mai yawa.
Har a fina-finai aka tsiri sanya Ajala, a fim dinsa na farko mai suna “White Witch Doctor”, ya samu $300 duk Mako. Sannan duk fina-finansa da sutturu irin na Afirika ya ke yinsu.
Ajala ya zagaye kasashe 87 a babur dinsa, a nan ne ya san manyan ‘yan siyasan kasashe kamar Gamal Abdul Nasser na Egypt, Jawarhalar Nehru na India, Mohammad Reza Shah Pahlavi na Iran, Ronald Reagan na Amurka, Abubakar Tafawa Balewa na Najeriya da sauransu.
Sai dai ya fara rayuwa mai dadi amma daga baya ya shiga cikin masifun rayuwa. Ya fara fuskantar kalubale bayan wata ma’aikaciyar jinya a Chicago ta ce ta haifa masa jariri a shekarar 1953, wanda ta sanya wa suna Oladipupo.
Olabisi ya ki amincewa da haifar yaron sai har an tabbatar da dansa ne ta hanyar gwajin asibiti, kuma ta amince amma sai ya tsere.
Bayan nan ne kotu ta yanke masa hukuncin biyan $10 duk sati. A wannan shekarar aka kama shi da laifin amfani da takardar banki ta bogi da kuma sata.
Duk da ya musa laifin, amma an yanke masa shekara 1 a gidan gyaran hali. Bayan ya fito, aka kara kama shi da laifin keta dokar dalibai, inda ya kamata yayi karatu a Santa Monica Junior College amma ba can yaje ba.
Bayan ya wuni a gidan rediyo yana bukatar a yi masa adalci. Ajala ya koma Amurka tare da matarsa Hermine Aileen a shekarar 1954, duk da aurensu bai yi wani karko ba, inda tayi ta zargin yana ha’intarta.
Ya kara aure bayan ‘yan watanni, inda ya auri wata jarumar finafinan turai, Joan. Daga baya ya koma Najeriya, saboda daukakarsa tayi ƙasa. Ya nemi hayar wani gida a Adeniran St. Bariga inda ya zauna tare da yaransa.
Bayan ciwo ya kama shi, kusan duk yaransa sun guje shi, ban da dansa Olaolu mai shekaru 20 da diyarsa Bolanle mai shekaru 17 a lokacin.
Ya mutu a babban asibiti da ke Ikeja a ranar 2 ga watan Fabrairun 1999 a cikin mawuyacin hali.
Comments
Post a Comment