Min menu

Pages

Wani gari a Najeriya da suke gayyatar macizai zuwa wajen bikinsu na al'ada.

 Wani gari a Najeriya da suke gayyatar macizai zuwa wajen bikinsu na al'ada.



Kamar yadda kowa ya sani Macizai guba ne a cikin al’umma, shi yasa ba’a kiwon su kusa da al’umma. Sai dai a cikin wannan rahoton, zamu kawo maku yadda dangantaka ta ƙullu tsakanin al’ummar Machina ta Jihar Yobe da kuma macizai.


 An bayyana cewa Macizan na kai ziyara ga mutanen garin na tsawon makonni musamman a lokutan bukukuwan al’ada.



 Machina na daya daga cikin kauyuka a jihar Yobe. Masarautar Machina kamar yadda ake ikirarinta tana da arzikin tarihi da al’adu. Wani abin al’ajabi da ke cikin garin mai tarihi shi ne yadda macizai da mutane suke mu’amala ba tare da cutar da junan su ba.


 Ba’a dai san lokacin da al’umar Machina da masarautar suka fara abota da macizai ba, amma wani abun mamaki shi ne yadda mutanen ke mutunta macizai, Kuma macizan suma suke mutunta ‘yan garin ta hanyar rashin cutar da kowa.


 Sai dai, hakan Ya samo asali daga wata tatsuniyar da ta shahara a tsakanin jama’ar garin cewa wata sarauniya ta haifi wasu tagwaye, wanda daya daga cikin su jariri ne, daya kuma maciji.


 Saboda haka, mutanen sun yi imanin cewa jinin sarauta yana gudana a cikin macizai a yankin. Don haka ne macizai suka yi mubaya’a ga fadar ta Machinama, inda ake zargin an haifi kakansu tare da daya daga cikin sarakunan kakanninsu, a matsayin ‘yan tagwaye.

Comments