Min menu

Pages

Wannan da kuke gani shekarunsa 27

 Wannan da kuke gani shekarunsa 27



Haƙiƙa a wannan duniyar da muke ciki akwai wasu cututtuka da ba a saba gani irin su ba, waɗanda ke shafar talakawa kuma suna barin su cikin mawuyacin hali.  Halin da Singh Manpreet ke ciki ke nan, wani matashi ɗan kimanin shekara 27 da aka haifa tun a shekara ta 1995 yayin da ya daina girma tun yana ɗan shekara ɗaya, nauyinsa ma bai wuce kilo 11 ba.  Maƙwabtansa a Hisar, ƙasar Indiya, suna kiransa da "Ƙaramin Mutum," kuma yana buƙatar kulawa ta sa'o'i 24, kasancewar yana abubuwa irin na ƙananun yara.


 Antinsa Lakhwinder Kaur, Yar kimanin shekaru 42, wadda suke zaune tare da Manpreet ita ce take kula da shi.  

 

 Manpreet ya tashi daga Mansa, Punjab, zuwa Hisar, inda yayi tafiya mai tazarar kilomita 112, saboda abokansa ba su yarda su kula da shi ba.  

 Kawunsa Karanvir Singh, mai shekaru 45, ya ce: “Manpreet na yin ɗabi'u irin na  ƙaramin yaro kuma a duk lokacin da yake cikin baƙin cikin yakan fashe da kuka haka idan yana cikin farin ciki yakan yi murmushi,” in ji kawunsa Karanvir Singh, ɗan shekara 45. Wanda ya kasance matashi mai ban sha'awa duba da yadda shi da matarsa suke kula da Singh Manpreet tamkar dan da suka haifa a cikin su.

  Mun shiga damuwa game da makomarsa, hakan tasa muka nemi shawara daga likitoci masu yawa, waɗanda suka bayyana cewa "ana buƙatar wasu makuɗan kudaɗe domin yi masa aiki."


 Kudin da sun kai kimanin dala $ 70,000. Kasancewar bamu da wannan kuɗin ne yasa muka nemi taimakon kungiyar GoFundMe sai dai har yanzu ba a samu adadin kuɗin da ake buƙata ba.  Manpreet yaro ne mai lafiya lokacin da aka haife shi, amma ya daina girma kafin ya iya tafiya ko magana, ba tare da wata alama ba.


 Lokacin da mahaifinsa, Jagtar Singh, mai shekaru 50, makiyayi mai tawali'u, kwararru suka gaya masa cewa ɗansa ya kamu da wata cuta wadda bazata barshi yayi girma ba, ya ji takaici.  Yana iya yiwa cewa batun sinadarai ne, a cewar likitoci.


  Iyalin Manpreet har yanzu suna cikin damuwa game da dalilin da ya sa ya daina girma, ganin cewa yana da babban yaya da ’yar’uwa da suka girma ba tare da wata matsala ba.


 MK Bhadu, jami'in asibiti ne, ya ce: "Saboda rashin daidaiton hormonal, hakan yasa ci gaban majiyyaci ya tsaya cak. Likitan ya ci gaba da cewa ya kamata iyaye su lura tun yaro yana da shekaru uku, su dinga saka masa idanu yadda ya kamata.  Idan jikinsa bai yi girma ba, ya kamata masu kula da shi su kai shi wurin da ya fi dacewa a yi masa magani.


 A kowane hali, masu bincike sun yi imanin cewa Manpreet ya kamu da wata cuta da ake kira Laron Syndrome, shi dai wannan ciwo mai wuyar magani ne, kuma ana tunanin zai iya shafar mutane 300 kawai a duniya.  Mafi akasarin mutanen da wannan cuta ta fi kamawa suna zaune ne a ƙauyuka  da kasashen yammacin duniya.

Comments