Kabilu mafiya kankanta da kuma karancin jama'a a Duniya.
Assalamu alaikum yan uwa barkanmu da wannan lokacin ya kuke ya hakurin kasancewa tare damu hakika muna matukar jin dadin yadda kuke kasancewa tare damu a koda yaushe muna godiya sosai da sosai a yau cikin shirin namu munzo muku ne da jerin wasu kabilu mafiya kankanta kuma wanda basu da jama'a sosai a Duniya.
Su dai wadannan kabilun bincike ya nuna ko kadan basu da yawa na mutane domin wasu gaba dayansu ma jama'ar dake cikin wannan kabilar basu haura dubu daya ba, Dan haka kai tsaye muje cikin shirin.
• Kabilar dogon:-kabila ce da take zaune a Mali da kuma wani yanki na kasar Burkina Faso, wannan kabilar an nuna tana da tarin mutane wanda yawansu baifi dubu dari uku zuwa dari biyar ko shida ba, itace kabila mai yawan jama'a cikin wannan bayanin da muke.
• Kabilar karamojong itama wata kabila ce da take Ethiopia amma ta matsa zuwa Uganda, tana da mutanen da basu haura dubu dari da doriya ba.
• Kabilar San wannan ma kabila ce wacce take da karancin mutane domin jama'ar cikin kabilar basu fi dubu dari da biyar ba, suna zaune ne a kasar Zimbabwe, Angola, Bostwana, Namibia.
• Kabilar Himba itama wannan kabilar karamar kabila ce wacce bata da mutane ko jama'a sosai domin duka yawan mutanen dake cikin kabilar basu haura dubu hamsin ba.
• Kabilar Sonoma ita ce yar karamar kabila mai karancin mutane domin duka yawan mutanen dake cikin kabilar basu fi dubu uku ba, suna zaune ne a wani yanki na kasar Uganda.
Comments
Post a Comment