Min menu

Pages

Kasashe 11 a Afrika da suka fi tara mutane masu ilimi abin mamaki babu Najeriya a cikin jerin.

 Kasashe 11 a Afrika da suka fi tara mutane masu ilimi abin mamaki babu Najeriya a cikin jerin.



Mujallar Africa Facts Zone, mai fitar da kididdiga kan lamuran da suka shafi nahiyar Afirka, ta wallafa jerin kasashe 11 da suka tara mafi yawan mutane masu ilimi.

 A cikin jerin, kasar Equatorial Guinea, ta ja ragamar tara dimbin al'umma masu ilimi da kashi 95 cikin 100. Sai kuma kasar Seychelles da ta biyo baya a mataki na biyu da kashi 94 cikin 100.

 Kamar yadda Africa Facts Zone ta kalato daga Hukumar Duniya mai bita a kan yawan jama'a, World Population Review, ta nuna cewa kasar Afrika Ta Kudu ce a mataki na uku da kashi 93 cikin 100. Sai kuma kasar Libiya a mataki na hudu da kashi 90 cikin dari na adadin mutanen kasarta da suka himmatu wajen neman ilimi. Mauritius ce a mataki na biyar, yayin da aka samu kashi 89 cikin 100 na adadin al'ummarta da suka mike tsaye wajen yakar jahilci. Sai dai abun mamaki shi ne, yadda Najeriya ba ta shiga cikin sahun kasashen ba da suka yi zarra a fannin ilimin boko. Abun mamakin shi ne yadda kasashe irinsu Bostwana, Zimbabwe, da kuma Gabon suka yi wa Najeriya fintinkau duk da kallon da ake mata a matsayin babban-goro cikin kasashen Afirka. Ga dai jerin kasashen 11 da kuma kashi-kashi na mutane masu ilimi da kowannensu ya kunsa:


1. Equatorial Guinea (95%) 

2. Seychelles (94%) 

3. South Africa (93%) 

4. Libya (90%) 

5. Mauritius (89%) 

6. Botswana da Burundi (87%) 

8. Cape Verde (85%) 

9. Zimbabwe (84%) 

10. Eswatini (83%) 

11. Gabon (82%).

Comments