Kasashen Africa 10 da suka fi kowacce kasa samun wutar lantarki.
Koda yake idan har kasa ta kasance kasa to akwai iyuwar akwai wutar lantarki, to saidai wata kasar bata da wutar lantarkin gamsashshiya, domin ko kadan bata isa a kasar domin ba'a kawo ta koda wanne lokaci wannan yasa sauran ma'aikatu da gidajen da suke da bukatar wuta suke sayen manyan injina ko kuma solar saboda karancin wutar.
Ku dauka kamar kasar Nijeriya duk da kasancewarta babba amma ko kadan basu da wutar lantarki wanda take isa, kusan koda yaushe babu wuta wannan yasa yan kasar suka fara hakura da duk wani abu indai na wutar lantarkin ne suka koma amfani da injina ko solar a gidajensu da kuma guraren aikinsu.
Duk da haka akwai wasu kasashe guda goma da su babu ruwansu da matsalar wuta domin suna samun wutar lantarkin sosai kuwa, sune zamu zayyano muku jerin su a kasa kamar haka:-
1. Mauritius 🇲🇺 (100%)
2. Tunisia 🇹🇳 (100%)
3. Egypt 🇪🇬 (99.8%)
4. Algeria 🇩🇿 (99.1%)
5. Morocco 🇲🇦 (99%)
6. Seychelles 🇸🇨 (99%)
7. Cape Verde 🇨🇻 (96.1%)
8. Gabon 🇬🇦 (90.7%)
9. Ghana 🇬🇭 (84.3%)
10. South Africa 🇿🇦 (84.2%).
Comments
Post a Comment