Manyan Kasashen duniya 10 da suka fi sauran kasashe arzikin man fetur a shekarar 2022
Ga jerin jaddawalin kasashe 10 da ke da arzikin mai, wanda kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta fitar. Jimillar arzikin mai a duniya an kiyasta ya kai ganga tiriliyan 1.48.
1. Venezuela
Ƙasar Venezuela tana samar da mai kimanin biliyan 304, sannan a kowace rana tana fitar da mai ganga 12,489.
2. Saudiyya
Ƙasar Saudiyya tana samar da mai kimanin biliyan 259,sannan a ko wacce rana tana fitar da ganga 11,545.7 na mai.
3. Iran
Ƙasar Iran tana samar da mai kimanin biliyan 209 wanda a kowacce rana tana fitar da ganga 3,538 na mai.
4. Iraqi
Ƙasar Iraqi tana samar da mai biliyan 145 sannan a kowacce rana tana fitar da ganga 2,986.6 na mai
5. Kuwait
Kasar Juwait tana fitar da mai kimanin biliyan 102,sannan a kowacce rana tana fitar da ganga 2,796.8 na mai.
6. Daular Larabawa
Daular larabawa tana iya samar da mai kimanin biliyan 98 sanan tana fitar da ganga 3,213.2 na mai a kowacce rana.
7. Rasha
Kasar Rasha tana samar da mai kimanin biliyan 80, wanda a kowacce rana tana iya fitar da mai kimanin ganga 10,397 a kowacce rana.
8. Libiya
Kasar Libiya ta na samar da mai biliyan 48,sannan a kowace rana tana fitar da mai ganga 1,483.
9. Najeriya
Najeriya tana da mai kimanin biliyan 37 sannan a kowacce rana tana fitar da mai ganga 2,524.1
10. Amurka
Kasar Amurka bata kasance kasa mai arzikin mai ba amma ta kasance kasar da take iya sarrafa mai wanda ya kai kimanin ganga Biliyan 47.
Comments
Post a Comment