Abubuwa 10 da za a rika tuna Yar'adua da su.
A rana 5 ga watan Mayu 2010, shekaru goma sha biyu da suka gabata ne tsohon shugaban Najeriya, Umaru Musa Yar' Adua ya rasu a kan mulki. Duk da cewa shekaru uku kawai ya yi a kan mulki gwamnatinsa ta dukufa wurin aiwatar da wasu ayyuka da tsare tsare inda wasu daga cikinsu an kammala su.
Ga dai jerin wasu abubuwa goma da za a rika tuna tsohon shugaban kasar da su kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa: Abubuwa 10 da za rika tuna Yar’adua da su.
1. Sakin kudaden kananan hukumomin jihar Legas Ba za a taba mantawa da marigayi Shugaba Yar' adua ba domin shine ya bayar da umurnin sakin kudaden kananan hukumomin jihar Legas ta tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya rike inda ya nuna kin amincewarsa a kirkirar Hukumar Cigaban Kananan Hukumomi (LCDA). Gwamnatin Obasanjo ta ki sakin kudaden duk da cewa kotu ta bayar da umurnin hakan.
2. Kirkirar shirin Afuwa da talllafi ga tsageran Neja Delta Yaradua ya kawo zaman lafiya a yankin Neja Delta ta shirinsa na yin afuwa ga tsegerun yankin muddin za su ajiye makamai. Masu tayar da kayan bayan sun yi amfani da damar da ya basu sun ajiye makamansu. Wannan abin ya yi sanadin samun cigaba a bangaren samar da man fetur da iskar gas a kasar. Hakan ne kuma ya yi sanadin kirkirar Maaikatar Neja Delta.
3. Bayyana kadarori A ranar 28 ga watan Yunin 2007, Yar’Adua ya bayyana wa duniya kadarorin da ya mallaka, shine shugaban kasa na farko da ya fara yin hakan a tarihin kasar. A lokacin ya bayyana cewa ya mallaki kadarorin da suka kai ₦856,452,892 ciki Naira Miliyan 19 na matarsa ne. Ya kuma bayyana cewa ana bin sa bashi na ₦88,793,269.77.
4. Bin dokokin kasa da biyayya ga hukuncin kotu A zamanin da ya ke mulki, ana yi wa marigayi Yaradua lakabi da "Mr Rule of Law" wato mai biyayya ga doka saboda mutunta hukuncin kotu da ya ke yi. A zamanin mulkinsa Jamiyyar People’s Democratic Party (PDP) mai mulki da rasa jihohi kamar Edo, Ondo, da Osun a kotu.
5. Kyakyawan alaka tsakanin bangaren zartarwa da bangaren masu yin doka Daya daga cikin abubuwan da za a rika tuna marigayi Yaradua da shi shine rashin yi wa juna katsalandan tsakanin bangaren zartarwa da masu yin doka. Wannan shine dalilin da yasa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya taba cewa marigayi Shugaba Yaradua dan siyasa ne da a zamaninsa ba samu rikici ba tsakanin bangaren masu yin doka da masu zartarwa.
6. Kwamitin yi wa dokokin zabe garambawul na Justice Mohammed Lawal Uwais Za kuma a rika tuna gwamnatinsa saboda kafa kwamitin Justice Mohammed Lawal Uwais na yin gyar ga dokokin zabe da za su taimakawa yadda ake gudanar da zabe a kasar idan an aiwatar da shawarwarin.
7. Seven-Point-Agenda A ranar 1 ga watan Augustan 2007, gwamnatin Yaradua ta sanar da wasu bangarori bakwai da za ta mayar da hankali a kai da suka da da Makamashi da lantarki, Samar da abinci, Yalwata arziki a kasa, Inganta Sufuri , Sauye sauye a bangaren filaye, Inganta tsaro da Ilimi.
8. Sauyi a kundin tsarin mulkin PDP domin kwace shugabancin kwamitin amintattu daga hannun tsaffin shugaban kasa Shi ne ya jagoranci yi wa kundin tsarin mulkin jamiyyar PDP garambawul ta yadda aka tsige tsohon shugaban kasa Oluesegun Obasanjo a matsayin shugaban kwamitin amintattu na jamiyyar.
9. Fadada manyan titunan Kubwa da na Airport road Gwamnatin tsohon shugaban kasa Yaradua ne ta samar da kudaden da aka yi amfani da su wurin fadada titin Kubwa da na Airport road da aka karasa aikin a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan. An sauya sunan Airport road zuwa maru Musa Yar’adua Expressway bayan kammala aikin.
10. Fadada Rafin Niger Gwamnatin marigayi Yaradua ta mayar da hankali sosai wurin aikin fadada Rafin Niger amma anyi watsi da aikin bayan rasuwarsa. Rafin Niger yana da matukar muhimmanci wurin inganta kasuwanci da tattalin arzikin arewacin Najeriya duba da cewa rafin ne zai hada kudanci da arewacin kasar.
Comments
Post a Comment