Jerin masallatai 4 mafiya kyau a Nigeria
Masallacin Bashir Uthman Tofa, Kano
Masallacin Bashir Uthman Tofa yana Gandun Albasa, Kano. Masallacinl yana da zane zane da gine-gine masu kyau matuka
kuma an yi shi da kyau da kayan aiki masu inganci . An sanya wa masallacin sunan Alhaji Bashir Uthman Tofa, dan takarar jam’iyyar Republican Convention (NRC) a zaben shugaban kasa da aka soke ranar 12 ga watan Yunin 1993 a Najeriya.
2 Babban Masallacin Kano,
An ce Mohammed Zaki ya mayar da shi wani sabon wuri a shekara ta 1582, kuma ya sake gina shi a wancan lokacin tsakanin 1855 zuwa 1883 da Sarkin Kano Abdullahi dan Dabo ya yi. Babban Masallacin na Kano, Bayan rushewarsa a a 1950s, Gwamnatin Burtaniya ta dauki nauyin gina sabon masallacin amatsayin hidima ga Najeriya.
3 Masallacin kasa na Abuja, wanda aka fi sani da National Mosque
Shi ne masallacin kasa na Najeriya. An gina masallacin ne a shekarar 1984 wanda yanzu haka kuma fitaccen malamin nan wato Prof Ibrahim maqari yake jagoranta masallacin.
4 Babban masallcin Ilorin dake jahar kwara
An gina babban masallacin na Ilorin a shekarar 1981. Masallacin babban wurin ibada ne yana cikin birnin Ilorin mai cike da hada-hadar jama'a, wanda ke da dimbin musulmi.
Comments
Post a Comment