Kasashe goma a Africa dake kan gaba wajen jin yaren turanci da kuma iya yin yaren
Nahiyar Africa ita ce ta biyu a yawan jama'a a duk fadin Duniya, kuma take da kabilu masu yawa da suke jin yaruka mabambanta.
Daga Cikin jerin yarukan da ake ji a Nahiyar, yaren turanci wato English ya dauki kaso mafi tsoka, domin ana yin yaren a kasashe masu yawa a fadin Nahiyar ta Africa.
Dan haka yanzu zamu kawo muku jerin wasu kasashe goma dake kan gaba wajen amfani da yaren na turanci.
• Nigeria ;- kasar Nigeria ita ce ta daya a duk jerin kasashen domin tanada mutane masu dimbin yawa da suke ni tare da iya yin magana da yaren.
Domin Nigeria tanada yawan mutane wanda suka haura miliyan 206, wanda daga cikin wadannan mutanen masu jin yaren na turanci sun kai miliyan 90 koma su haura.
• Uganda:- Idan maganar yawa ake, zance na gaskiya Uganda adadin mutanen ta basu da wani yawa da za'a iya kira sosai domin da kyar zasu haura miliyan miliyan 46.
To saidai duk da haka suna da mutane masu ji da kuma yin magana da yaren turanci wanda yawansu yakai miliyan 29.
• South Africa :- Ita kasar south Africa tana da yaruka masu yawa to amma mafiya yawa daga cikin mutanen suna jin yaren na turanci.
• Zambia :- Kasar Zambia itama mafiya yawa daga cikin mutanen dake kasar suna jin yaren turanci sannan suna iya yin magana dashi.
Sauran kasashen sune irinsu:-
√ Ghana
√ Bostwana
√ Kenya
√ Zimbabwe
√ Malawi
√ Rwanda
Wadannan sune jerin kasashen da suke kan gaba wajen yin magana da yaren na turanci, wasu ma daga cikin kasashen turancin shine a matsayin official language dinsu.
Comments
Post a Comment