Min menu

Pages

Shugabannin kasashen Afirka 6 da suka gaji kujerun mulki a wajen mahaifansu

 Shugabannin kasashen Afirka 6 da suka gaji kujerun mulki a wajen mahaifansu


Ba kasafai ake gadon mulkin ko mukamin siyasa ba kamar yadda akan samu irin wannan tsari a masarautu a kasashen duniya.

Amma kuma akwai daidaikun kasashe musamman a nahiyar Afirka da ke mayar da mulkin siyasa a matsayin wani abu da akan gada daga iyaye ko kaka da kakanni.

Ga bayanan wasu daga cikin shugabannin kasashen Afirka da suka gaji kujerun mulkin daga mahaifansu:


1. Joseph Kabila- Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo



Joseph Kabila Kabange ya shugabanci kasar Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo daga watan Janairun shekarar 2001 zuwa Janairun shekarar 2019.

Ya kuma hau kejerar shugabancin kasar ne kwanaki goma bayan kisan gillar da aka yi wa mahaifinsa Shugaba Laurent-Désiré Kabila.

An haifi Mista Joseph Kabila, a ranar 4 ga watan Yunin shekarra 1971, a lardin Sud-Kivu, jami'an soja ne kuma dan siyasa.

Kabila, wanda da ne ga jagoran 'yan tawaye na kasar ta Congo Laurent Kabila, ya girma ne tare da yin karatu a kasar Tanzania.

Yana cikin dakarun 'yan tawaye da suka taimaka wa mahaifinsa korar Shugaba Mobutu Sese Seko na kasar Zaire in 1997.

Bayan da aurent ya zama shugaban kasar ne ya sake dawowa da kasar sunanta na ainihi wato Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, kuma daga nan ne aka tura Joseph kasar China don kara samun horon aikin soja.

Bayan dawowarsa gida ne aka nada shi a matsayin babban hafsan sojin kasar da matsayin manjo janar.

Ba dadewa ba ne a shekarar 1998 aka fara kalubalantar Laurent Kabila kan mulkin danniya da ayyukan 'yan tawaye wanda hakan ya fadada da ya sa aike wa da dakaru daga kasashen Afirka da dama.

Bayan kisan Shugaba Laurent ne aka nada Joseph a matsayin sabon shugaban kasar a ranar 26 ga watan Janairun shekarar 2001.

Ya kuma gaji dimbin matsaloli na yake-yake da suka dabaibaye kasar, kana akasarin yankunan sun kasance babu gwamnati ko wasu muhimman abubuwa, da tattalin arzikin ya durkushe saboda yawan tashe-tashen hankula.

Duk a cewa Joseph Kabila ya yi ta fafutika a bangaren maido da zaman lafiya, amma ya rika cin karo da masu adawa.

A shekarar 2004 ne aka yi zargin yunkurin yi masa juyin mulki, amma dakaru masu goyon bayan sa suka dakatar.

Kabila bai yi kasa a gwuiwa ba a kokarin da yake yi na hada kawunan al'ummar kasar.

Bayan da aka sake sabon fasali a kundin tsarin mulkin kasar a shekarar 2002 aka gudanar da zabuka masu jam'iyu da dama irinsa na farko a cikin shekaru arba'in.

Amma kuma Kabila ya gaza samun kuri'u mafi rinjaye, sai dai ya kayar da abokin takararsa Jean-Pierre Bemba a zaben raba gardamar da aka yi cikin watan Oktaoban shekarar 2006.

A farkon shekarar 2008 ne Kabila ya rattaba hannun yarjejeniyar zaman lafiya da kungiyoyin 'yan tawaye 20 da ke fada a yankin gabashin kasar, amma daga yarjejeniyar ta wargatse inda wasu 'yan tawayen suka sake komawa ruwa.


2. Faure Gnassingbé - Togo




An haifi shugaba Faure Essozimna Gnassingbé Eyadéma a ranar 6 ga watan Yunin shekarar 1966, kuma dan siyasa ne da ya kasance shugaban kasa tun a shekarar 2005.

Kafin zama shugaban kasarta Togo, mahaifinsa shugaba Gnassingbé Eyadéma ya taba ba shi mukamin Minista daga shekarar 2003 zuwa 2005.

Bayan mutuwar shugaba Eyadéma ne a shekarar 2005, aka yi gaggawar nada Gnassingbé a matsayin sabon shugaban kasa tare da goyon bayan sojoji.

Amma kuma shakku game cancanta a bisa kundin tsarin mulkin kasar ya haifar da gagarumar matsin lamba a kan Gnassingbé.

Ya kuma lashe zaben shugaban kasa mai cike da ce-ce-ku-ce a ranar 24 ga watan Afrilun shekarar 2005, kuma an rantsar da shi a matsayin shugaban kasa.

A shekarar 2010 ne aka sake zabar Gnassingbé a matsayin shugaban kasa karo na biyu.

Bayan da jami'iyun adawa suka ki amincewa da zaben ne kasar ta fada cikin munanan tashe-tashen hankula lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da raba dubbai daga muhallansu.


3. Mahamat Idriss Déby - Chadi




Sabon shugaban kasar Chadi Mahamat Idris Deby janar din na soja ne wanda bai wuce shekara 40 ba, da ya maye gurbin kujerar shugabancin kasar bayan mutuwar mahaifinsa shugaba Idris Deby Itnu a ranar 20 ga watan Afrilun shekarar 2021.

An haifi Janar Mahamat Idriss Déby a 1983 inda ya zama ɗaya daga cikin 'ya'yan marigayi Idriss Deby.

Ana kuma yi masa lakabi da Mahamat Kaka, saboda a hannun kakarsa ya taso.

A lokacin da mahaifinsa ya mutu, shi ne shugaban dakarun da ke tsaron shugaban kasar. 

A 2009, Mahamat Idriss Deby ya halarci yakin da Am Dam, wanda aka fafata da wani dan uwansa Timan Erdimi, da ke zama ɗan ɗan uwan tsohon shugaban ƙasar, a gabashin Chadi.


4. Ali Bongo Ondinba - Gabon




Shugaba Ali Bongo Ondimba ɗa ne ga tsohon shugaban kasar ta Gabon Omar Bongo, wanda ya shugabanci kasar daga shekarar 1967 har ya zuwa lokacin rasuwarsa a shekarar 2009.

Ya kuma kasance shugaban kasar Gabon na uku tun daga watan Oktobar shekarar 2009, bayan rasuwar mahaifinsa .

An kuma haife shi a kasar Gabon Ali Bongo da aka fi sani a da Alain Bernard Bongo a kasar Congo-Brazzaville makwabciya a watan Fabrairun shekarar 1959.

Shekarunsa takwas kacal a lokacin da mahaifinsa Omar Bongo ya zaman shugaban kasa a shekarar 1967, kamar yadda wani masanin tarihi a kasar Faransa François Gaulme ya shaida.

Rayuwar Shugaba Ali Bongo cike take da ce-ce-ku-ce musamman ma a lokacin da yana karami zuwa matashi.

Ko a haihuwarsa ma sai da aka rika ce-ce-ku-ce - jita-jitar da a kodayause yake musantawa ta ci gaba da yaduwa har zuwa tsawon shekaru a kan cewa an dauko shi riko ne daga Najeriya a yankin kudu maso gabashi a lokacin yakin basasar kasar.

Wasu na daukarsa a matsayin wani batacce, mai neman mata da ke alfahari da irin arzikin man da kasar Gabon ke da shi a matsayin kamar gadon gidansu.

Wata rashin lafiya da ya samu kansa ciki a shekarun baya ta haifar da damuwa a kasar, inda har sai da sojoji suka yi yunkurin yi masa juyin mulki - wanda bai sa mu nasara ba.

Cikin dalilansu kuwa sun hada da kokarin maido da kasar a hanyar dimokaradiyya madaidaiciya bayan da aka gudanar da zaben shkearar 2016, wanda Bongo ya sha da kyar, da kuma aka bayyana cike yake da magudi da tarzoma.


5. Muhammed Bin Sidi Alaouite na Moroko

An haifi Sarki MuhammEd Bin Sidi Alaouite na Morocco a ranar 21 ga watan Agustar shekarar 1963, a Rabat babban birnin kasar.

Ya kuma hau karagar sarautar kasar ne a ranar 23 ga watan Yulin shekarar 1999 bayan mutuwar mahaifinsa Sarki Hassan na biyu.

Ba da jimawa ba ne da hawansa kan karagar mulki, Sarki Mohammed VI ya yi wa kasa jawabi ta kafar talabijin cewa shawo kan matsaloli na talauci da cin hanci da rashawa ta hanyar samar da ayyukan yi da inganta bangaren kula da kare hakkin biladama.

Amma kuma, wasu daga cikin sauye-sauyensa sun fusata masu tsattsauran kishin Islama, tare da samun suka daga Musulmai masu ra'ayin rikau.

A cikin watan Fabrairun shekarar 200 ne ya kafa sabuwar dokar iyalai ko Mudawana, wacce ta tanadi kara wa mata karfin gwuiwa.

A cikin watan Disambar shekarar 2020, ne Sarki Mohammed VI ya amince da karfafa dangantaka da Isra'ila a bisa yarjejeniyar cewa Amurka za ta san da zaman yankin Yammacin Sahara a karkashin ikon kasar Morocco.


6. Sarki Mswati III na Eswatini

Sarki Mswati III (Makhosetive) ɗa ne ga Sarki Sobhuza II wanda daya daga cikin amarensa Ntfombi Tfwala ta haifa masa.

An haife shi a ranar 19 ga watan Afirilun 1968 a Manzini.

An nada shi yariman Mswati III, Ingwenyama, sannan daga bisani aka nada shi Sarkin Swaziland a ranar 25 ga watan Afirilu 1986 a lokacin yana da shekara 18 a duniya, don haka ya zama sarki mafi kankantar shekaru a duniya a wannan zamanin.

Sarki Sobhuza II ya rasu a ranar 21 ga watan Agusta 1982, masu zabar sarki wato (Liqoqo) suka zaɓi Yarima Makhosetive a matsayin sabon sarki.

Comments