Wani Dutse daya shafe shekaru 65 yana ci da wuta
Abun mamaki wani dutse kenan da ake kira (Yanar Dagh) dake kasar Azarbaijan wanda ya kwashe shekaru 65 yanaci da wuta.
Koda yake ba abin mamaki bane daga lamarin ubangiji domin shine yake iya yin komai a lokacin da yaga dama kuma shine yake tafiyar da komai.
A yau zamu kawo muku wani Dutse mai abin mamaki wanda aka ce yayi shekaru 65 yana ci da wuta.
Shidai wannan dutse mai abun mamaki mai suna Yanar Dagh ance wata gobara ce ta iskar gas take ci gaba da ci ajikinsa tsawan shekaru 65 ba tare da ta lafa ba. Shidai wannan dutsen yana wani tsauni ne dake gabar tekun Absheron dakuma Tekun Caspian dake kusa da garin Baku, babban birnin kasar ta Azarbaijan.
Masu bincike sunce harshen wutar dake ci a acikin dutsen ya tashi sama a cikin iska kusan nisan mita 3.
azihiri babu wanda yasan dalilin wannan wutar dake ci na tsawan shekaru 65
ana kiran kasar Azarbaijan da kasar wuta sabo da wannan dutsen.
.
Comments
Post a Comment