Wani kogi wanda yake dafa duk halittar data fada cikinsa saboda tsananin zafinsa.
Ga bayanin yadda ruwan kogin yake
Koda yake abu ne mai wahala mutane su yadda damu idan mun fada ko kuma mun kawo labarin wani abu mai matukar abin mamaki, wasu kai tsaye suke karyatawa ba tare da sunyi bincike ba.
To amma tunda mu gaskiya muke fada baza mu daina kawo muku labarai irin wannan na abubuwan mamaki da al'ajabi ba, yau cikin shirin namu munzo muku ne da labarin wani kogi mai matukar abin mamaki wanda yake dafa duk abinda ya shiga cikinsa ba tare da wani bata lokaci ba, wannan ruwan wani ruwa ne da shi kadai yake daukar zafi domin wani lokacin har tafarfasa za kuga yana yi shi kadai saboda tsananin zafin da yake dashi. Anyi ittifakin cewa wannan ruwan zai iya dafa duk abinda ya fada ciki ba tare da wani bata lokaci ba.
Wannan yasa aka zayyana kogin a daya daga cikin kogi mafiya hatsari a Duniya, kuma mai abin mamaki duk da cewa akwai wasu daga cikin kogunan da suma suke da abin mamaki misali kamar na kasar Tanzania wanda yake daskarar da duk halittar data taba ruwansa.
Wannan kogin sunansa shanay timpishka da yake kasar Peru, wannan gurin mutane da yawa sunje kuma sun tabbatar da cewa haka ruwan gurin yake yana da tsananin zafi kuma yana iya dafa abubuwan da suka fada ciki.
Ga duk mai son ganin asalin kogin daga gurin mutanen da suka je gurin Kai tsaye ga Link nan zamu ajiye zai kaishi har gurin.
Wawa ke gardama, ku kuma yakamata ku riƙa haƙuri damu saboda ba a taru aka zama ɗaya ba
ReplyDelete