Min menu

Pages

Wasu sababbin abubuwa guda 7 mafiya ban mamaki a Duniya

 Wasu sababbin abubuwa guda 7 mafiya ban mamaki a Duniya



Ko Kun San Sababbin Abubuwa Bakwai Mafiya Ban Mamaki A Duniya?

Akwai sababin abubuwa bakwai da suka fi ban mamaki a Duniya, wanda hakan wani kokari ne na kirkiro wasu abubuwan ban mamaki domin su maye gurbin tsofaffin, kasancewar shida daga cikin bakwan na tsofaffin sun bace, abin da ya yi saura kawai ita ce Dalar Giza da take Kasar Misra.


Sakamakon haka ne ya sa aka shirya wata hanya ta kada kuri’a ga duk Duniya, ta amfani da na’ura mai kwakwalwa, a karkashin wata kungiya mai zaman kanta ta musamman da ake kira (New Open World Corporation) a Turance. To bayan an kada kuri’ar ne aka sanar da abubuwan da suka sami nasara a ranar 7 ga Yuli, 2007 a birnin Lisbon dake kasar Portugal.



Abubuwan da aka sanar a karshen zabe a matsayin mafi kololuwar abubuwan ban mamaki da dan Adam ya gina da hannunsa su ne; Na farko shi ne Ginin Taj Mahal na kasar Indiya, Na biyu Kasaitacciyar katangar kasar Chaina, wadda aka fi sani da suna “Great Wall of China’’ a Tutance.



Sai kuma abu na uku shi ne, Mutum mutumin Yesu al-Masihu dake Kasar Brazil, Wanda aka fi sani da suna “Christ the Redeemer’’ a Turance. Sai kuma abu na hudu, Wani Birni dake kan tsauni da ake kira (Machu-picchu) a Kasar Peru.


Daga shi sai kuma Birnin da ake kira da suna (Chichen Itza ) wanda aka gina a siffar dala a Kasar Medico. Na shida kuwa, Gidan Tarihi na Petra da ke birnin Jordan. Cikon na bakwai, Sai hamshakin Dakin Taro dake birnin Rum a Kasar Italiya, Wanda aka fi sani da “Colosseum’’ a Turance. Wadannan dai su ne abubuwa bakwai da aka yarda da cewa dan’Adam ya nuna gwaninta wajen gina su a wannan Duniya tamu.


Wannan kungiya dai ta kasar Swiss da ta gudanar da wannan zabe, ta sanarwa da Duniya cewa, an kada kuri’u fiye da miliyan 100 ta hanyar Yanar Gizo wato Internet, da kuma ta wayar Tarho. Ko da dai an kira wannan zabe da cewa ba sahihi bane saboda ba’a samar da wata kariya da za ta hana wani mutum ya kada kuri’a fiye da sau daya ba. To amma dai sun tabbatar da cewa wadanda aka zaba din sune aka sanarwa da Duniya.

Comments