Min menu

Pages

Jerin kasashe 10 na duniya da mutanen kasashen sukafi tsawan rayuwa.

 Jerin kasashe 10 na duniya da mutanen kasashen sukafi tsawan rayuwa.



 1. Hong Kong itace kasa ta farko a duniya da mutanenta sukafi tsawan rayuwa  inda  mata suna kai shekaru 87. maza na kaiwa  82  a duniya


2. Japan tana da matsayi na biyu mafi tsawan  rayuwa a duniya she shine   87.7 ga mata suna kaiwa shekaru 87 yayin da maza akasar suke kai  shekaru 81 a duniya 


  


 3. Macau Macau, yanki ne  na musamman na kasar Sin wato china , yana da matsayi na uku mafi girma na tsawon shekaru . Maza na iya tsammanin za su rayu na kimanin shekaru 81.3  mata za su iya tsammanin rayuwa na kimanin shekaru 87.2 


4. Switzerland ita ce  Ƙasar Turai ta farko a cikin jerin kasashe masu matsakaicin tsawon rayuwa a duniya. Ana sa ran mata za su rayu na kimanin shekaru 85.   6 sannan kuma maza za su kai kimanin shekaru 81.9. 


5. Kasar Singapore tana da matsayi na biyar mafi  tsawon shekaru a duniya  abin mamaki  shine  mata suna da tsawon rai fiye da maza, saboda ana sa ran za su rayu shekaru 85.8 yayin da ake sa ran maza za su kai shekaru 81.6. 


6. Kasar  Spain a kasar Spain mata na rauyawa kalla  shekaru 86.3 yayin da maza akasar na rayuwa akalla na shekaru  80.9   An san Spain da cin abinci na Mediterranean, wanda al'ummarta ke gani a matsayin babban dalilin da ya sa suke  wannan tsawon rai. 


 7. Italiya Tana  da matsayi na bakwai na  mafi tsawan  rayuwa a duniya ƙasar, Italiya mata na tsammanin za su rayu na tsawan shekaru 85.6   yayin da maza a kasar na rayuwa a kasa ko sama da shekaru 81.4 


 8. Australiya mata  a Ostiraliya na iya tsammanin za su rayu matsakaicin shekaru 85.4 yayim da  maza kuma  na iya tsammanin za su rayu shekaru 81.6. 


9 Kasar Israel  a wannan kasa ta Isra'ila maza na iya rayuwa na tsawon shekaru akalla  81.1 yayin da mata a kasar ke rayuwa akalla na tsawan shekaru 84.4


10 kasar  Iceland  kasar   Iceland shine na goma mafi girma a duniya ana sa ran mata za su rayu fiye da maza a Iceland, tare da matsakaicin tsawon rayuwa na shekaru 84.5 yayin da maza a kasar zasu rayu na  shekaru 81.6.

Comments