Masallatai uku mafiya girma a Duniya.
Kamar yadda kowa ya sani masallaci guri ne tsarkakekke kuma mai daraja wanda musulmi suke gabatar da ibada a cikinsa.
Duk wani musulmi ya aminta da masallaci a matsayin gurin bautawa ubangiji wanda ya halicci kowa da kuma komai shine mamallakin sammai da kassai.
Dan haka zamu kawo muku jerin wasu masallatai guda uku da aka bayyana sunfi kowanne masallaci girma sannan da daukar tarin mutane dan haka muje cikin shirin.
1 Masallacin harami:- Wannan shine masallaci na farko kuma mafi girma da yake a garin makka, kuma shine masallaci mafi daraja a Duniya baki daya, haka kuma shine masallaci guda daya da yafi tara mutane domin yana daukar mutane sama da miliyan hudu.
2 Masallacin Annabi SAW dake Madina:- Ko tantama babu wannan shine masallaci na biyu a Duniya wajen daraja da kuma girma, sannan kuma wajen tarin jama'a domin yana daukar mutane sama da miliyan biyu.
3 Masallacin Karachi dake Pakistan:- Cikin masallatan da aka bayyana sunfi girma a Duniya, Masallacin Karachi shine yazo na uku. Yana kasar Pakistan ne sannan kuma yanada bangarori guda uku a cikinsa.
Yana daukar mutane sama da miliyan daya.
Comments
Post a Comment