Wasu mutane da ake nemansu ruwa a jallo saboda ta'addancinsu
Nima kaina abin da ya bani mamaki da naga kusan dukkan mutanen da ake nema ruwa a jallo a Duniya saboda an ayyana su a matsayin yan ta'adda wai dukansu musulmai ne da suka fito daga kasashen musulmai.
Ban gane nufin turawan nan ba da ko kadan basa saka sunan wasu daga cikin mutanen su a matsayin yan ta'adda duk da tarin ayyuka na ta'addanci da sukayi sai suka tare wasu kalilan daga cikin musulmi suka ce sune yan ta'adda.
Wannan abinda kalilan daga cikin mutanen mu sukai yasa kasashen duniya na kafirai suke mana kudin goro tare da ce mana yan ta'adda gaba daya.
Wadannan da zan zayyano ko zan kawo a kasa sune jerin mutanen da ake nema ruwa a jallo saboda ta'addancinsu da kuma abubuwan da suka aikata a Duniya.
• Oumar albashir shine shugaban kasar sudan an ayyana shi cikin jerin mutanen da ake nema ruwa a jallo kamar yadda kasashen yamma suka ce.
• Ayman Al-Zawahiri shine shugaban yan alqa'ida wanda yake iyaka da pakistan da kuma afghanistan ance ana nemansa ne saboda yace zai dauki fansar musulmi bisa abubuwan da arna sukai musu sannan yana so ya hada daular musulunci ta zama daya a cewar binciken.
• Aboubakar al-bagdadi shima yana daga cikin wanda aka bayyana ana nemansa wai ance shima na daga cikin jerin mutanen dake tada husuma domin yace zai kafa daula ta musulci a cewar binciken.
• Ibrahim Al-Asiri shima wani dan kasar yemen ne ana nemansa ruwa a jallo saboda shine yake yin boma bomai
• Abubakar Shekau mutum dan Nijeriya daya takurawa cikin gida dama sauran kasashen dake ketare da kashe kashe da sunan yin jihadi a cewarsa wai karatun boko babu kyau dan haka yake kafirtar da duk wani wanda yai karatun boko.
Wadannan sune kadan daga cikin wadanda ake nema a duniya saboda abubuwan da suka aikata wasu ma inaga sun mutu wasu kuma an rasa inda suke.
Hakika wadannan sun aikata laifika idan aka bincika amma bai dace ana yiwa musulmi kudin goro ba dan wasu kalilan daga cikinsu sun aikata aikin daya sabawa doka.
Sannan ina mamakin yadda ba'a fadi sunan arne ko guda daya ba duk kuwa da cewa idan anyi bincike sun fimu yawan yan ta'adda domin har yanzu cikin wadannan babu wanda yai laifin hitler.
Comments
Post a Comment