Min menu

Pages

Kofar da idan aka fice ta cikinta ba'a dawowa ( The door of no return )

 Kofar da idan aka fice ta cikinta ba'a dawowa ( The door of no return )



Wannan wata kofa ce wacce idan mutum ya fice ta ciki bazai taba dawowa ba ya tafi kenan ( The door of no return) sunanta.

Dalilin da yasa aka sanyawa wannan kofar sunan shine ta cikinta ake fitar da duk wasu da aka kama yan Africa zuwa turai a matsayin nayi.


Kofar tana kasar Senegal a tibirin goree, mafiya yawan yan Africa sunbi ta cikin wannan kofar hannu da kafarsu daure da sasari inda turawa suka dauke su a matsayin bayi shekaru 400 da suka wuce .



Duk lokacinda mutum ya fice ta cikin kofar nan to shikenan yayi bankwana da yan uwansa da sauran danginsa ko yana so ko baya so.

Gaba daya rayuwar yan Africa ta baci a wannan lokacin, domin mutane da yawa sun zama bayi ko mutum baya so dole zai hakura ya zama bawa kenan a gurin turawa, za azo da mutum a wuce dashi ta wannan kofar.


Domin ta wannan kofar sukai ta ficewa da mutanen da suka kama a matsayin bayi a wancan lokacin.


Wannan dalilin yasa aka sanyawa wannan kofar door of no return.


Hakika wannan kofar tanada dimbin tarihi agun yan Africa domin an zaluntar dasu kafin a wuce dasu ta cikin wannan kofar.

Comments