Min menu

Pages

Kudaden kasashen da suka fi daraja a Africa

 Kudaden kasashen da suka fi daraja a Africa



Kowa dai yasan yadda kudaden Nahiyar Africa suke kasancewa wajen rashin daraja idan aka hadasu da darajar dollar ko kuma Euro, wani lokacin sai kuga darajar dollar din ta ninka darajar wasu kudaden na Africa kamar kasar Zimbabwe ko kuma kasar Nijeriya inda yanzu dollar din farashin ta har ya haura dari shida.


To saidai duk da haka akwai wasu kasashen da kudin kasarsu yake da daraja sosai harma yana yin gogayya da farashin dollar din duk da baikai dollar din ba.


Dan haka ga jerin kasashen da kudin nasu yake da daraja sosai fiye da sauran kasashen.

Kasa ta farko wanda kudinta yake da daraja a Africa itace Tunisia domin Tunisian dinar 3.096 shine yake a matsayin dollar daya .



Kasa ta biyu ita ce kasar Libya wacce suke amfani da kidinsu Libyan dinar wanda 4.84 yake daidai da dollar daya.



Sai kuma kasa ta uku ita ce kasar Ghana inda kudinsu Ghanian cedi 8.046 yake daidai da dollar daya.



Wadannan dai sune ƙasashen da kudinsu yafi na kowacce kasa daraja a Africa.

Ku bayyana mana ra'ayinku 

Comments