Min menu

Pages

Mutumin da ya daga hannunsa na dama bai sauke ba har tsawon shekaru 45

Mutumin da ya daga hannunsa na dama bai sauke ba har tsawon shekaru 45



Assalamu alaikum yan uwa barkanmu da wannan lokacin, sannan sannunmu da sake haduwa daku a cikin wani sabon shirin.

Yau cikin shirin namu munzo muku da labarin wani mutum wanda ya daga hannunsa na dama sama kuma bai sauke ba har tsawon shekaru 45.


AMAR BHARATI shine asalin sunansa, amma mutane suna masa lakabi da mai hannu a dage.


Tsawon Lokaci AMAR yana dage da hannunsa na dama sama ba tare da ya sauke ba saboda wani dalili nasa.


Kamar yadda labari yazo dashi ance Amar Bharati yayi aiki a wata ma'ajiyar dukiya a wancan lokacin wanda yanzu muke kiran gurin da sunan banki a shekarar 1970  sannan yanada aure tare da yara.


Lokaci guda Amar Bharati ya yanke shawarar barin iyalansa tare da sauran danginsa gaba daya tare da aikinsa domin yaje yai aikin da zai bar tarihi, ya bar komai nasa na jin dadi tare da sauran abubuwa na debe kewa ya ta tattara komai nasa ga wani gunkinsu da suke kira Shiba.


Abin baizo wa da amar da sauki ba a farkon marra, na ganin ya gaza samo abinda zaiyi domin ya samu karbuwa ga wannan gunki daga karshe dai ya yanke shawarar ya kawo wani abu da idan yayi zai samu kusanci ga wannan gunkin da suka dauke shi abin bautar su.


A shekarar 1973 Amar ya yanke shawarar ya daga hannunsa har zuwa tsawon lokacin da zai gama sauran rayuwarsa .


Wannan abinda yayi zaisa ya zama wani tauraro wanda za ana zuwa kallonsa a ko ina a cikin duniya.


Amar ya sake fadin dalilinsa na daga wannan hannun shine domin a kalubalanci yawan yake yaken da ake, burinsa a kawo zaman lafiya a duniya baki daya da kuma girmama gunkinsa.


Lokacin da Amar ya fara daga hannunsa yaji ba dadi kuma abin yazo masa wani iri domin har ciwo gurin ya fara yi masa amma duk da haka bai sauke ba haka har ya fara daina jin ciwon bayan tsawon wani lokacin domin duka jijiyoyin gurin sun daina aiki.


A takaice dai babu abinda Amar yafi so face zaman lafiya a kuma kawar da yake yake wannan yasa ya dunkule hannunsa da niyyar sauran mutane suyi koyi dashi a zauna lafiya a duniya.


Wannan kenan mu hade daku a wani sabon shirin mun gode.










Comments