Min menu

Pages

Wasu Daga Cikin Abubuwan Da Aka Haramta A Dokar Ƙasar Koriya Ta Arewa

 Wasu Daga Cikin Abubuwan Da Aka Haramta A Dokar Ƙasar Koriya Ta Arewa



1- Fita ƙasashen waje neman magani


A bisa dokar ƙasar Koriya ta Arewa an haramtawa kowa tafiya wata kasar  domin neman magani na kowacce cuta saidai ka yi jinya a cikin gida duk tsananin cutar da take damun ka saboda wannan dokar ta su ta hana tafiya ƙasashen waje shugaban ƙasarsu sai da ya yi shekara 7 cif-cif bai taɓa zuwa ko da makwanciyar ƙasarsa da sunan ziyara ko halartar wani taro ba. 


2- Siyan Mota


A bisa dokar dokar ƙasar Koriya ta Arewa ba kowa yake da ikon siyan ko mallakar mota ba saidai idan kai hamshaƙin attajiri ne ko kuma babban ƙusa a gwamnati, ita ma motar baka isa ka siyi mai lumfashi ba. A bisa kiyashi, a cikin mutane dubu mutum ɗaya ne za ka ga ya mallaki mota a kasar. 


3-  Addini


A bisa dokar ƙasar  Koriya ta Arewa kowanne addini haramtacce ne sai na su na gargajiya, dan haka ba ka da ikon gudanar da wani shagalin biki daya jiɓinci wani addini. Bugu da ƙari, Ba a siyar da littaffan addinai a duk faɗin kasar.


4- Ba a saka shuɗin wando( Blue jeans)


A kasar Koriya ta Arewa ba a saka shuɗin wando(blue jeans) saidai ka saka baƙi ko wani launin. Bugu da ƙari idan zaka yi shiga ba a yarda kayi kamar ta turawa sak ba. 


5- Mata ba saka takalmi mai tsini


A bisa dokar ƙasar Koriya ta Arewa an haramtawa mata saka takalmi mai tsinin gaske saidai su saka mai ɗan tudu


6- Aski


A kasar Koriya Ta Arewa ba kowanne irin aski aka yarda mutum ya yi ba, dan haka gwamnati ta ware aski ga kala 15 ga maza sannan guda 18 ga maza, duk shagon askin daka je saidai ka/ki zaɓi daya daga cikin su ayi maka/ki


7- Lemon Coca-Cola


Gwamnatin ƙasar ta haramtawa shaguna siyar da lemon coca-cola saidai su ma suna da irin na su lemokan na cikin gida. Dan haka ta zama ƙasa ta biyu bayan ƙasar Cuva wacce ta ɗauki irin wannan matakin. 


8- Waya/Salula


Ba kowanne mutum aka lamuncewa ya mallaki waya a ƙasar ba. Sannan wayar Apple( iphone) an haramtawa a'ummar ƙasar amfani da ita. A bisa ƙiyasi a  cikin mutane miliyan 15 , mutane miliyan ɗaya ne suke da waya a kasar. 


9- Yanar gizo-gizo


A ƙasar Koriya ta Arewa an haramta amfani da yanar gizo-gizon daya haɗe duniya wato website ko ziyartar sauran shafukan sada zumuntar zamani idan ka ga an amincewa mutum ya ziyarcesu saidai babban mutum amma suna dasu na cikin gida a ƙasar. 


10- Ba a kira zuwa kasashen ƙetare


A bisa dokar Koriya ta Arewa ba a yarda ka  kira wani mutum dake wata kasar ba, dan haka ne a shekarun baya aka kashe mutane akalla 9 saboda an samesu da laifin kiran waya zuwa ƙasashen ketare. Dan haka idan ka ziyarci ƙasar akwai layin waya na musamman da zaka siya domin ka kira ƙasarku


11- Talabijin


A ƙasar Koriya ta Arewa babu gidajen talabijin da mutum zai kalla sai gidajen talabijin guda 4 rak! da gwamnati ta amince a  haska a kasar.


12- Jaridun ƙasashen ketare


Ba a siyar ko karanta duk wata jaridar ƙasashen ketare sai ta cikin gida wacce gwamnati ita ce take faɗar abin da za a wallafa domin al'ummar kasar su karanta. 


13- Ƙunzugun mata(Always) 


Mata a ƙasar basa amfani da ƙunzugun mata na al'ada(Always) saidai su yi amfani da ɗan diras


14- Maziyarta ƙasar


Duk wanda ya ziyarci ƙasar Koriya ta Arewa duk ida zai je yana karƙashin kulawar gwamnati , dan haka za a haɗaka da jami'in tsaro ya ke ba ka kulawa. Sannan ba a yarda ɗauki wani hoto da zai nuna al'ummar ƙasar suna cikin ƙunci ko wahalar rayuwa ba idan ka yi haka za a ɗauke ka a matsayin wanda ya ci amanar ƙasa. Da sauran dokokin da za a gindaya maka.


15- Tsarin Iyali


A haramta duk wani tsarin iyali a ƙasar, daidai da amfani da kondom haramun ne. 


16- Haramta Dariya Ko Nuna Alamun Farin Ciki A Wasu Kwanaki


A ranar 17 ga watan Disamba na shekarar 2021, gwamnatin ƙasar Koriya ta Arewa ta sakawa ƴan ƙasarta takunkumi ko haramcin yin dariya, shan giya, cefane da gudanar da duk wani shagulgulan biki kamar na aure ko na zagayowar ranar haihuwa.


Wannan dokar an saka ta ne domin tunawa da tsohon shugaban ƙasar daya rasu wato Kim-Jong-il wanda ya cika shekaru 10 da rasuwa. Wanda kuma ya shugabanci ƙasar daga shekarar 1994 zuwa 2011. Kana daga baya ɗansa na uku wato Kim-Jong-Un ya maye gurbinsa.


Dan haka, ya zama al'ada a ƙasar,  duk ranar 17 ga watan Disamba na kowacce shekara al'ummar ƙasar suna gudanar da zaman makokin jimami ko alhali na tunawa da tsohon shugaban ƙasar.


Saidai kuma a wannan shekarar shugaban ƙasar Kim-Jong-Un ya bayyana haramta yin dariya ko murmushi, shan giya, biki, siyayya, ko nuna duk wata alama da za ta nuna kana cikin farin ciki, har na tsawon kwanaki 11.


Duk wanda kuma aka same shi da laifin aikata ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan zai fuskanci hukunci mai tsauri.


Sannan akwai sauran dokokin da bamu ambata ba bayan waɗannan.


Turkashi! Ka ji ɗan Najeriya, hakiƙa mu godewa Allah da Ya yi mu a Najeriya ba a Koriya ta Arewa ba domin ina da yaƙinin idan muka kwatanta rayuwarmu da tasu sai mu ga tamkar a Aljannar duniya muke.

Comments